Ba a taba zabe na gaskiya kamar na 2019 ba a tarihin kasar Najeriya – Gwamnan jihar Niger

Ba a taba zabe na gaskiya kamar na 2019 ba a tarihin kasar Najeriya – Gwamnan jihar Niger

- Gwamnan jihar Niger, Abubakar Bello ya ce ba a taba zabe na gaskiya kamar na 2019 ba a tarihin kasar Najeriya

- Bello ya ce zuwa kotu da Atiku yayi ba sabon abu bane

- Gwamnan ya fadi hakan ne a lokacin da ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa inda suka yi ganawar sirri

Gwamna Abubakar Bello na jihar Niger ya bayyana zaben 2018 a matsayin zabe mafi gaskiya da amana da aka taba gudanarwa a tarihin Najeriya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar Shugaban kasa bayan wata ganawar sirri tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ba a taba zabe na gaskiya kamar na 2019 ba a tarihin kasar Najeriya – Gwamnan jihar Niger
Ba a taba zabe na gaskiya kamar na 2019 ba a tarihin kasar Najeriya – Gwamnan jihar Niger
Asali: UGC

Sani Bello ya bayyana cewa babu wani sabon abu game da tafiya kotu da dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar yayi don neman kotu ta sake duba lamarin saboda kowa na da yancin bin ra’ayin kansa.

Kan dalilinsa na ziyartan fadar Shugaban kasa, Sani Bello yace: “Na zo ne domin na taya Shugaban kasa murnar lashe zabe da yayi, shima ya taya ni murna kuma ina yi masa fatan alkhairi. Mun taya juna murna sannan mun tattauna abubuwa na sirri.”

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Gwamnatin jihar Niger tace kudaden da za a kasha wajen gyare-gyaren gidan gwamnatin jihar zai kai kimanin naira biliyan 3.2.

KU KARANTA KUMA: Sake zabe: IGP ya tura manyan jami’ai 23 domin sanya idanu a mazabu a fadin kasar

Kwamishinan ayyuka, Zakari Jikantoro ya bayyana hakan ga manema labarai a Minna, babbar birnin jihar a jiya Alhamis, 21 ga watan Maris.

Yace ayyukan an raba su ne a rukuni daban-daban, inda ya kara da cewar an kammala aiki akan rukunin farko wanda ya ci kimanin naira biliyan 2.1; yayinda aka bayar da kwangilan na biyu wanda ya kai kimanin naira biliyan 1.6.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel