Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Mai martaba Sarkin Patigi ya rasu

Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Mai martaba Sarkin Patigi ya rasu

Mai martaba Sarkin masarautar Patigi, na jahar Kwara, Alhaji Ibrahim Chatta Umar ya rigamu gidan gaskiya a ranar Talata, 19 ga watan Maris bayan yayi fama da gajeriyar jinya, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito fadar sarkin Ilorin mai martaba Sulu Gambari shugaban majalisar sarakunan jahar ce ta sanar da mutuwar Sarkin Patigi, kamar yadda hadimin Sarkin, Muritala Raheem ya bayyana.

KU KARANTA: Kashe kashe a Zamfara: Buhari da Yari sun goga gemu da gemu a Villa

Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Mai martaba Sarkin Patigi ya rasu
Marigayi Sarkin Patigi
Asali: UGC

Kafin rasuwarsa, Sarkin Patigi ne mataimakin shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta jahar Kwara, kuma ya rasu ne a wani Asibiti dake babban birnin tarayya Abuja, ana sa ran gudanar da jana’izarsa a ranar Laraba, 20 ga watan Maris da misalin karfe 2 na rana a garin Patigi.

Shima Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari ya bayyana kaduwarsa game da mutuwar Sarkin Patigi, wanda ya bayyanashi a matsayin mutum mai mutunci da kowa ke ganin girmansa, yace an tafka babban rashin da maye gurbinsa zai yi wuya.

Bugu da kari Sarki Sulu Gambari ya bayyana mamacin a matsayin mutum mai son zaman lafiya, tare da yin duk mai yiwuwa wajen ganin jama’a sun zauna lafiya, hakanan mutum ne dake son ganin cigaban al’ummarsa.

Daga karshe Sarki Gambari yayi addu’ar Allah Ya jikan mamacin, tare da fatan Allah Ya yi masa sakayya da gidan Aljanna Firdausi, haka nan Sarkin yayi addu’ar Allah ya baiwa iyalansa hakurin rashi, da ma al’ummar Patigi gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel