Zahra Buhari ta saki sabbin hotuna, ta rubuta wasu muhimman abubuwa game da kanta
Zahra Buhari-Indimi ta sanya wasu masu amfani da shafin zumunta da dama shauki bayan ta saki wasu kyakwawan hotuna nata dauke da wasu sakonni akan yadda ta ke son kanta da alfahari da al’adarta.
Kyakyawar yar Shugaban kasar kuma mahaifiya ga tillon danta ta kasance ma’abociyar kwalliya da iya ado wanda hakan kan burge yan Najeriya da dama. A sabbin hotunan da ta saki kwanan nan, Zahra tayi Magana game da abun alfaharinta a matsayinta na yar Najeriya wacce ke tsaye kan mafarkinta.
Ta rubuta: “Ina nada kambi na kamar wanda aka yi daga kwal da lu’u-lu’u, amma abunda aka yi wannan kambi da shi yafi gaban haka. Addinina, al’adda... da komai da yayi ni, wacce nake a yau shine ashon wannan kambi.
"Shine katin shaida na. Yar Najeriya, yar arewacin Najeriya, uwa, mata, diya kuma yar’uwa. Kuma babu wani abu, ina nufin babu wani abu da zai tsaya ga mafarkina, In shaa Allah. #defyingthenorms #defyingthestereotypes #defyingthenormsnorth"
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta rufe babban cibiyar nan na kasuwanci a Lagas
A hoton karshe ta rubuta: “A wannan lokaci ina rera taken alkawarin Najeriya ne da babban murya sannan na ji duk wata kalba da nake furtawa a jikina. Sannan a zuciyata na san cewa ina daukarwa Najeriya alkawari da dukkan zuciyata. Kaima kayi?"
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng