Uwargidar gwamnan kebbi ta biya wa wata mata da ke tsare a gidan yari tarar N15,000

Uwargidar gwamnan kebbi ta biya wa wata mata da ke tsare a gidan yari tarar N15,000

Uwargidar gwamnan jihar Kebbi, Dr Zainab Atiku Bagudu ta biya wa wata mata da ke tsare a gidan kurkuku tarar naira 15,000.

Hajiya Zainab ta ce akwai wani shiri nata na biya wa fursunoni tara wanda take yi tare da hadin gwiwar Kungiyar lauyoyi mata ta Najeriya da wasu kungiyoyin. a kuma bayyana cewa bisa ga al'ada su kan kai ziyara gidajen yari don biyan tarar sannan kuma a irin wannan ziyarar ne a daya da cikin gidajen yarin da ke jihar Kebbi ta ga wannan mata.

Ta ce ta ga mata uku a daure kuma wannan matar ta fi daukar hankalinta kasancewa tana rike da 'yar jaririyarta.

Uwargidar gwamnan kebbi ta biya wa wata mata da ke tsare a gidan yari tarar N15,000
Uwargidar gwamnan kebbi ta biya wa wata mata da ke tsare a gidan yari tarar N15,000
Asali: UGC

Ta kara da cewar da ta yi bincike sai aka bayyana mata cewa an yanke wa matar daurin wata shida ne ko kuma biyan naira 15,000 saboda fada da ta yi da makwabciyarta.

Dr Zainab ta biya kudin tarar tare da sa mutanen da ke yi mata aiki su yi wa matar rakiya har gida.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta mika ta’aziyyar ta ga iyalen wadanda rushewar gini ya cika da su a Legas

An tattaro cewa matar dai ta fi wata daya a daure kafin biyan tarar.

Misis Bagudu ta ce talauci na daya daga cikin abubuwan da ke haddasa tashin hankali a wasu yankunan karkara a Najeriya.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa a ranar juma'a ne kotun koli ta tabbatar da kwacen wucin gadi da babbar kotun jihar Legas tayi na kudi Naira biliyan 2.4 wanda ake zargin mallakin matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Misis Patience Jonathan.

Bai wuce sati daya ba kenan da kotun kolin ta tabbatar da kwace dala miliyan 8.4 wanda mallakin tsohuwar uwar gidan shugaban kasan ne tare da umartar ta da ta bayyana gaban babbar kotun jihar Legas din don bayyana dalilan da zasu hana gwamnatin tarayya mallake kudin na ang dindindin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel