Iko-sai-Allah: Mace mai shekara 65 ta haifi yarinya a Abuja

Iko-sai-Allah: Mace mai shekara 65 ta haifi yarinya a Abuja

Tabbas ikon Allah da yawa yake kuma yakan faru a kowane lokaci, kuma a kowane wuri kamar dai yadda muka samu labarin wata mata mai shekara 65, Uwargida Comfort Timothy dake a garin Abuja da ta haifi jaririya mai koshin lafiya, bayan ta shafe shekara 18 tana neman haihuwa ba.

Majiyar mu ta Aminiya dai ta binciko mana cewa Madam Comfort ta yi auren fari ne tun a shekarar 2001 amma bata samu haihuwa ba, duk da cewa bata saduda ba, ta yi ta addu’a tare da azumi a kai-a kai, domin Allah ya ba ta haihuwa.

Iko-sai-Allah: Mace mai shekara 65 ta haifi yarinya a Abuja
Iko-sai-Allah: Mace mai shekara 65 ta haifi yarinya a Abuja
Asali: UGC

KU KARANTA: Za'a kara gina rijiyoyin mai 37 a Najeriya

Aminiya ta gana da mijin matar, wanda yake cikin murmushi da farin ciki, ya ce wannan yarinya da suka haifa, ta kasance abin al’ajabi daga Allah kuma yana godiya ga Allah da Ya albarkace su da samunta.

Iyayen jaririyar sun sanya mata suna “Ayobami” wanda haka ke nufin “Farin Ciki Ya Zo.” Sun shawarci sauran magidanta da ke fuskantar rashin haihuwa da su karfafa imani da Allah kuma su ci gaba da addu’a ba gajiyawa.

To mu sai dai muce Allah ya ci da sauran ma'autan da ke neman haihuwa a duk inda suke a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel