Yusuf Buhari ya taka wani mataki na harkar karatun boko

Yusuf Buhari ya taka wani mataki na harkar karatun boko

Da namiji daya kwal ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari ya kammala aikin yi ma kasa hidima wanda aka fi sani da suna National Youth Service Corp, NYSC, a turance, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Legit.ng ta ruwaito batun kammala bautan kasa na Yusuf ya tabbata ne daga wani hotonsa daya karade shafukan sadarwar zamani, musamman Facebook, inda yake sanye da kayan bautan kasa dauke da takardar shaidar kammala bautan kasa.

Yusuf Buhari ya taka wani mataki na harkar karatun boko (Hoto)
Yusuf Buhari
Asali: Facebook

KU KARANTA: Jama’an Ganduje da na Abba gida gida sun gudanar da addu’o’in samun nasara a zaben Kano

Yusuf ya dauki wannan hoto ne a wani daki dake gidansu afadar gwamnatin tarayya dake babban birnin tarayya tare da yayansa, Alhaji Musa Haro Daura, da ga yayar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Idan za’a tuna a shekarar data gabata ne Yusuf tare da kanwarsa Zahra Buhari suka kammala karatunsu na digiri a wata jami’ar Birtaniya, inda bayan dawowarsu Najeriya ne Zahra tayi aure, yayin da Yusuf kuma ya shiga bautan kasa.

Haka zalika a kimanin shekaru biyu da suka gabata babbar diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen uwargidarsa Aisha Buhari, Halima, ta kammala karatun kwarewa a harkar zama cikakken lauya mai lasisi.

Yusuf Buhari ya taka wani mataki na harkar karatun boko (Hoto)
Yusuf Buhari
Asali: Facebook

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da nada kwamitin da zata tsara yadda za’a gudanar da bikin rantsar dashi karo na biyu a matsayin shugaban kasar Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu.

Buhari ya nada sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a matsayin wanda zai jagoranci wannan muhimmin kwamitin, kamar yadda sanarwa daga ofishin babban sakataren ayyukan gama gari, Olusegun Adekunle ya nuna.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Ministan al’adu da watsa labaru, Lai Muhammed, Ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau, Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, Ministan Abuja, Muhammed Bello, da shugaban jam’iyyar APC ta kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel