Mata sun mamaye ofishin INEC Sokoto, sun bukaci a sanar da Tambuwal ya ci zabe

Mata sun mamaye ofishin INEC Sokoto, sun bukaci a sanar da Tambuwal ya ci zabe

Wasu mata guda uku da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bawa mukamin kwamishina sun jagoranci mata wajen yin zanga-zangar lumana a ofishin hukumar zabe ta kasa (INEC) da ke Sokoto a yau, Talata, da rana.

Matan uku; Farfesa Aisha Madawaki, Dakta Kulu Abubakar da Hajiya Kulu Sifawa, sun jagoranci zanga-zangar ne domin tilasta INEC ta bayyana sunan Tambuwal a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar gwamna da aka yi ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Sun bayyana cewar rashin bayyana Tambuwal a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar rashin adalci ne.

A cikin matan da su ka mara wa kwamishinonin wajen gudanar da zanga-zangar akwai shugabar matan jam’iyyar PDP, Hajiya Rabi Iyawa, da Hajiya Jamila Bafarawa; matar tsohon jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa, da kuma Hajiya Fatima Illo; shugabar hukmar ilimin bai daya (UBE) a jihar Sokoto da kuma ragowar wasu matan ma su dumbin yawa.

Mata sun mamaye ofishin INEC Sokoto, sun bukaci a sanar da Tambuwal ya ci zabe
Tambuwal
Asali: UGC

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta (INEC) ta bayyana zaben kujerar gwamna da aka yi ranar Asabar da ta gabata a jihar Sokoto a matsayin wanda bai kammalu ba.

Baturiyar zabe a jihar, Farfesa Fatima B. Mukhtar, ce ta bayyana da duku-dukun safiyar yau, Litinin, bisa hujjar cewar adadin kuri’un da aka soke ya fi adadin banbancin kuri’un da ke tsakanin ‘yan takarar biyu.

DUBA WANNAN: Rikicin jihar Taraba ya kara zafi, an kara tsaurara doka hana jama’a fita

Kamar yadda sakamakon zaben na karshe ya nuna, jam’iyyar PDP ta samu nasara da adadin kuri’u 489,558 yayin da jam’iyyar APC ke biye ma ta da adadin kuri’u 486,145.

An fafata a matakin kujerar gwamna a jihar Sokoto tsakanin gwamna mai ci, Aminu Waziri Tambuwal na jam’iyyar PDP, da babban abokin hamayyar sa, Ahmad Aliyu na jam’iyyar APC.

75,403 ne adadin kuri’un da aka soke daga mazabu 136 da ke fadin kananan hukumomin jihar Sokoto 22, kamar yadda baturiyar zaben ta sanar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel