Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano, CP Wakili ya zama gwarzon zaben 2019

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano, CP Wakili ya zama gwarzon zaben 2019

- Alhaji Mohammed Abdullahi Sugar, ya ce kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano, Mohammed Wakili, shi ne ya zama gwarzon zaben wannan shekarar ta 2019

- Suger ya ce ya kamata Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, Mohammad Adamu ya ware kwamishinan domin bashi kyautar girma

- Ya bukaci sauran jami'an rundunar 'yan sanda da ke a fadin kasar da su yi koyi da CP Wakili, yana mai cewa ba aikinsu bane kare kusoshin gwamnati

Alhaji Mohammed Abdullahi Sugar, ya ce kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano, Mohammed Wakili, wanda aka fi sani da 'Maza kwaya - Mata kwaya', shi ne ya zama gwarzon zaben wannan shekarar ta 2019.

Sugar, wani abokin siyasar dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a zaben da aka kammala, ya ce ya kamata Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, Mohammad Adamu ya ware kwamishinan domin bashi kyautar girma.

Ya ce kwamishinan ya kasance mai nuna adalci a yayin gudanar da ayyukansa ga fararen hula, musamman yadda ya bada dama ga kowanne bangare a zaben ya baje kolinsu ba tare da nuna tsangwama ga jam'iyyar hamayya ba.

KARANTA WANNAN: Fuskokin wasu mutanen da suka samu nasarar lashe zaben gwamnoni a jahohin su

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano, CP Wakili ya zama gwarzon zaben 2019
Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano, CP Wakili ya zama gwarzon zaben 2019
Asali: Facebook

Ya bukaci sauran jami'an rundunar 'yan sanda da ke a fadin kasar da su yi koyi da CP Wakili, yana mai cewa ba aikinsu bane kare kusoshin gwamnati, sai dai kare martaba da kuma 'yan cin dan Nigeria ba tare da duba matsayi ba.

Ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa bayan sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar, inda ya ce hakan ya tabbatar da cewa Atiku ne ya lashe zaben shugaban kasa a jihar amma jam'iyyar APC ta murde sakamakon zaben domin baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari damar sake lashe zabe a karo na biyu.

"Atiku ya samu nasara a Kano da ma sauran manyan jihohi a kasar nan. An zabe shi a ko ina, amma an murde zaben domin Buhari ya samu nasara. Sai dai, muna fatan cewa zamu kwato 'yancin mu da aka sace mana a cikin kotu," a cewarsa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel