Bana kaunar mu fara yar tsama da yan majalisa – Inji Buhari

Bana kaunar mu fara yar tsama da yan majalisa – Inji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana fatan samun kyakkyawar alaka da zamantakewa da sabbin yan majalisun dokokin Najeriya da aka zaba da zasu kafa sabuwar majalisa ta tara, musamman wajen lamurran da suka shafi kasafin kudi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne ta bakin Kaakakinsa, Malam Garba Shehu a ranar Litinin, 11, ga watan Maris a babban birnin tarayya Abuja, inda yace yana fatan a mayar da kasafin kudi yana aiki tsakanin watan Janairu zuwa Disamba.

KU KARANTA: Zaben gwamna: APC ta lashe jahohi 13, PDP ta samu nasara a jahohi 7

Bana kaunar mu fara yar tsama da yan majalisa – Inji Buhari
Buhari da abokansa
Asali: Facebook

Shugaban kasa ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakoncin tsofaffin abokansa da suka yi makaranta tare, wadanda suka ziyarceshi domin tayashi murnar sake lashe zabe a gidansa dake garin Dauran jahar Katsina.

A jawabinsa, Buhari ya bayyana damuwarsa game da yadda tsaikon da aka samu wajen kammala aiki akan kasafin kudin daga bangaren majalisar ya janyo tasgaro ga yadda gwamnati take aiwatar da ayyukanta.

Sai dai Buhari yace yana fatan ta sauya zani a wannan lokaci, tunda dai jam’iyyar APC ce keda rinjaye a duka majalisun biyu da suka hada da majalisar dattawa, da kuma majalisar wakilai.

Daga karshe Buhari ya gode ma abokannasa da suka kawo masa ziyara, wanda suka yi makarantar Katsina Middle School a shekarar 1953, da suka je a karkashin jagorancin Sanata Abba Ali.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel