APC da PDP na tseren dab-da-dab a Lagas, Kano, Kaduna da Sokoto

APC da PDP na tseren dab-da-dab a Lagas, Kano, Kaduna da Sokoto

Ana tabka gumurzu a tsakanin yan takarar jam’iyyar Progressives Congress (APC) da na Peoples Democratic Party (PDP) a jihohi irin su Kano, Lagas, Sokoto da kuma Kaduna a zaben gwamnoni da ya gudana a jiya Asabar, 9 ga watan Maris.

Sakamako daga mazaubu a jihohin da zabe ya gudana ya nuna cewa manyan jam’iyyun siyasar na tseren dab-da-dab.

Sai dai ba wai an kammala hada kuri’un bane kuma ba a wai an san wanda yayi nasara bane a yanzu haka.

APC da PDP na tseren dab-da-dab a Lagas, Kano, Kaduna da Sokoto
APC da PDP na tseren dab-da-dab a Lagas, Kano, Kaduna da Sokoto
Asali: Depositphotos

Har yanzu ana ci gaba da hada kuri’u a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Jami’an hukumar zabe na jiha ne za su sanar da gwamnonin da suka yi nasara a kowace jiha bayan an kammala hada sakamakon zabe a fadin jihohin.

Zabe ya gudana ne a jihohi 29 cikin 36 na kasar. Hakazalika a jiyan ne aka gudanar da zaben yan majalisun jihohi.

KU KARANTA KUMA: Zabe: An gano asirin da magauta su ka yiwa El-Rufa’I asiri a Kaduna

A baya Legit.ng ta rahoto cewa jiya Asabar, dan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar adawa ta PDP, Abba Kabir Yusuf, ya tsallake rijiya da baya biyo bayan wani mummunan farmaki na masu ta'ada a tsaka da zaben gwamnoni da na yan majalisun dokoki na jiha.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Haruna Abdullahi, shine ya jibinci shaidar da wannan mummunan lamari yayin ganawar sa da manema labarai na kafar watsa labarai ta Channels TV a jiya Asabar cikin babban birni na Kanon Dabo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

\Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel