Yar’ uwar Shugaba Buhari mai shekaru 84 ta yi tafiyar mita 100 don yin zabe

Yar’ uwar Shugaba Buhari mai shekaru 84 ta yi tafiyar mita 100 don yin zabe

- Babbar yayar Shugaban kasar Muhammadu Buhari, Hajiya Rakiya Adamu-Amadodo ta gudanar da aikin da ya rataya a wuyanta a matsayinta na yar kasa mai yanci

- Rakiya mai shekaru 84 yi tattaki har tsawon mita 100 da kafa domin yin zaben gwamna da na majalisar jiha

- Ta samu rakiyar jikarta da kuma wasu abokan arziki

Hajiya Rakiya Adamu-Amadodo, babbar yayar Shugaban kasar Muhammadu Buhari da ta rage a ranar Asabar, 9 ga watan Maris ta gudanar da aikin da ya rataya a wuyanta a matsayinta na yar kasa mai yanci inda ta kada kuri’ arta na zaben gwamna da majalisar dokoki.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Daura ta ruwaito cewa yar’ uwar Shugaban kasar ta yi tafiyar mita 100 a kafa zuwa mazabar Kofar Baru 002 da ke Daura domin yin zabenta da misalin karfe 12:34 na rana.

Yar’ uwar Shugaba Buhari mai shekaru 84 ta yi tafiyar mita 100 don yin zabe
Yar’ uwar Shugaba Buhari mai shekaru 84 ta yi tafiyar mita 100 don yin zabe
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa Adamu-Amadodo ta samu rakiyar jikanta, yan’ uwa da abokan arziki zuwa wajen zaben.

Akalla mutane 854 aka yiwa rijista a mazabarta.

KU KARANTA KUMA: Kai-tsaye: Yadda zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi ke gudana a Nasarawa, Niger da Kwara

Da farko Legit.ng ta rahoto cewa Shugaba Muhammadu Buhari da safiyar Asabar ya kada kuri'arsa a Kofar Baru, PU 003 dake garin Daura, jihar Katsina. Ya kada kuri'arsa ne tare da uwargidarsa, Hajiya Aisha Buhari misalin karfe 8;04 na safe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel