Buhari ya gina katafaren Masallaci mai cin mutane 1000 a kauyen iyayensa (Hotuna)

Buhari ya gina katafaren Masallaci mai cin mutane 1000 a kauyen iyayensa (Hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani katafaren Masallacin Juma’a daya gina a kauyen iyayensa, Dumurkul dake garin Daura na jahar Katsina, a ranar Juma’a, 8 ga watan Maris.

Legit.ng ta ruwaito daruruwan jama’a ne suka halarci bude Masallacin juma’an, daga cikin har da mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, tare da sauran shuwagabannin al’umman Musulman garin Daura.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta ari bakin mijinta: Yayan jam’iyyar APC kadai zamu raba ma mukamai

Buhari ya gina katafaren Masallaci mai cin mutane 1000 a kauyen iyayensa (Hotuna)
Masallacin
Asali: UGC

A jawabinsa, Sarkin Daura, Alhaji Faruk ya jinjina ma iyalan shugaba Buhari game da ginin Masallacin, musamman yadda suka bayar da filin gonarsu wanda akansa aka gina Masallacin, sa’annan a bayyana ginin Masallacin a matsayin manuniya ga yadda Buhari ke son jama’ansa.

Haka zalika mai martaba Sarki ya gode ma al’umman garin Daura da yan Najeriya da suka sake zaben Buhari a karo na biyu don cigaba da jan ragamar mulkin Najeriya, sa’annan ya nemi su bashi duk gudunmuwar da yake bukata.

Shima a jawabinsa, babban limamin Masallacin, Alhaji Sulaiman Dusti ya yi addu’an Allah ya taimaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma ya kareshi daga sharrin masharranta.

Daga karshe Liman Sulaiman ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari daya tabbata ya sauke nauyin dake rataye a wuyansa tare da yin kira a gareshi daya cika dukkanin alkawurran daya daukan ma yan Najeriya, kuma ya sani Allah zai tambayeshi akan duk abinda yayi.

A wani labarin kuma, uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta shawarci gwamnatin jam’iyyar APC da kada ta kuskura ta sanya bare a cikin wadanda zata raba ma mukaman siyasa, matukar ba yayan jam’iyyar APC bane.

Aisha ta bayyana haka ne a yayin wani liyafar cin abinci da ta shirya a garin Daura na jahar Katsina don murnar samun nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda tace lokaci yayin daya kamata a sakanka ma yan jam’iyya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel