Kai ma za ka ga soyayya tsagwaron ta – Hadimin Buhari ya yiwa masoyin Buhari albishir

Kai ma za ka ga soyayya tsagwaron ta – Hadimin Buhari ya yiwa masoyin Buhari albishir

Bashir Ahmad, mai taimaka wa shugaba a bangaren sadarwar zamani, ya yabi matashin nan, Aliyu Mohammed Sani, da ya wanka tare da shan ruwan kwatami don murnar cin zaben Buhari tare da yi ma sa albishiri din cewa shi ma zai ga soyayya zalla.

Da ya ke bayyana hakan a cikin wani rubutu da ya yi a shafin san a Tuwita, Bashir ya ce, “na yi magana da shi a yau, yana nan a raye cikin koshin lafiya kuma insha Allah rayuwar sa za motsa zuwa mataki nag aba kamar yadda ta dukkan ‘yan Najeriya za ta motsa. Soyayya ce ta sa ya aikata hakan kuma shi ma zai ga soyayya zalla.”

A daya daga cikin labaran Legit.ng kun karanta cewar Aliyu Mohammed Sani, matashin da ake yada jitar-jitar cewar ya mutu bayan ya yi iyo tare da kwankwadar ruwan kwatami a Bauchi, yana nan daram da rai da lafiyar sa.

Da ya ke Magana da wakilin jaridar Daily Trust ta wayar tarho a jiya, Laraba, Sani ya ce labarin da ake yada wa a dandalin sada zumunta cewar ya mutu ba gaskiya ba ne.

Kai ma za ka ga soyayya tsagwaron ta – Hadimin Buhari ya yiwa masoyin Buhari albishir
Aliyu Mohamme Sani
Asali: UGC

Sani, mai sana’ar fenti, ya yi watsi da jita-jitar cewar an garzaya da shi asibiti bayan ya kwankwadi ruwan kwatar.

Sani ya ci al washin yin wanka tare da kwankwadar ruwan kwata matukar shugaba Buhari ya sake lashe zabe.

DUBA WANNAN: Dahiru Bauchi: Shugaban kungiyar Izala ya fasa kwai a kan wasikar kulla yarjejeniya da El-Rufa'i

Sai dai kalaman hadimin na Buhari sun jawo ma sa kakkausar suka daga 'yan Najeriya da ke ganin cewar bai kamata a yabi duk wanda ya aikata irin abinda Sani ya yi ba.

Salon murnar cin zabe Buhari da Sani ya jawo cece-kuce daga jama'a da dama.

A cewar sa, ya sha ruwan kwatami tare da yin iyo a ciki domin cika alkawarin da ya dauka a gaban dumbin jama’a cewar zai yi hakan idan Buhari ya ci zabe.

Da gaske ne na dauki alkawarin yin hakan kafin a yi zabe, na cika alkawarin da na dauka kuma ban a nadamar abin da na aikata,” matashin ya fada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel