Sabon rikici ya barke a Kogi: An kashe mutane 7, an kona gidaje

Sabon rikici ya barke a Kogi: An kashe mutane 7, an kona gidaje

An kashe a kalla mutane bakwai tare da kone gidaje 50 a wani sabon rikicin kabilanci da ya barke a garuruwan Sheria da Oguma da ke karamar hukmar Bassa a jihar Kogi.

Majiyar mu ta shaida ma na cewar rikicin ya barke ne da sanyin safiyar yau, Alhamis, tsakanin kabilun Egbura Mozum da Bassa Kwomu.

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne su ka kai harin a kan al’ummar garuruan Sheria da Oguma da sanyin safiyar yau, lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane da asarar dukiya.

Majiyar mu ta sanar da mu cewar yanzu haka jama’ar garuruwan da dama sun tsere daga gidajen su a yayin da ake cigaba da zaman dar-dar a yankin.

Sabon rikici ya barke a Kogi: An kashe mutane 7, an kona gidaje
Gwamnan jihar Kogi; Yahaya Bello
Asali: UGC

William Aya, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Kogi, ya tabbatar da labarin kai harin tare da bayyana cewar sun gano gawar wani mutum guda daga cikin wadanda aka kasha yayin harin.

Ya ce an sanar da DPO na ofishin ‘yan sanda da ke Bassa kuma ba tare da wani bata lokaci bay a aike da jami’ai domin shawo kan lamarin.

DUBA WANNAN: Ban mutu ba, ina nan da rai da lafiya ta – Matashin da ya yi iyo a kwata saboda Buhari

Ya kara da cewar an kai gawar wani mutum da ba a san ko waye ba asibiti domin gudanar da gwaji na musamman a kan ta.

Aya ya ce kwamishinan ‘yan sanda a jihar Kogi, CP Hakeem Busari, ya aike da Karin wata rundunar ‘yan sanda zuwa yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel