Katafaren kamfanin sarrafa tumatir na Dangote dake jahar Kano ya fara aiki

Katafaren kamfanin sarrafa tumatir na Dangote dake jahar Kano ya fara aiki

Katafaren kamfanin sarrafa tumati da fitaccen attajirin nan Alhaji Aliko Dangote ya bude a garin Kadawa na jahar Kano ta fara aiki ganga ganga, bincike ya nuna a duk nahiyar Afirka babu wata kamfanin sarrafa tumatir da ta kai wannan girma.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kamfanin, Malam Abdulkareem Kaita ya bayyana cewa kamfanin dake sarrafa tan dubu daya da dari biyu (1,200tons) na danyen tumatir ya fara aiki bayan kammala duk wasu shirye shirye da tsare tsare.

KU KARANTA: Waka a bakin mai ita: Yadda na kashe mai horas da kungiyarmu– Inji Dan kwallo

Katafaren kamfanin sarrafa tumatir na Dangote dake jahar Kano ya fara aiki
Katafaren kamfanin sarrafa tumatir na Dangote dake jahar Kano ya fara aiki
Asali: UGC

Malam Kaita yace kamfanin ta shiga yarjejeniya da manoman tumatir dake yankin, inda suka amince akan karancin farashin da zasu dinga sayar da tumatir ga kamfanin, da haka yace sun magance matsalar samun tumatir.

“Mun cimma yarjejeniya da wasu jiga jiga manoman tumatir guda uku, mun amince zamu dinga saye akan farashin da ake sayarwa a kasuwanni, amma za’a dinga sake duba farashin bayan duk kwanaki biyu, kuma zuwa yanzu bamu samu wata matsala dasu ba.” Inji shi.

Bugu da kari shugaban kamfanin ya tabbatar ma jama’a cewa babu wani tumatir da aka sarrafa daya kai na Dangote inganci, sakamakon yana dauke da kashi 100 na zallan tumatir, don haka yayi kira ga gwamnati data hana shigo da tumatir daga kasashen waje don bunkasa aikin sarrafa tumatir a gida.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel