Majalisar dokokin Adamawa ta rasa dan majalisa karo na biyu a cikin mako guda

Majalisar dokokin Adamawa ta rasa dan majalisa karo na biyu a cikin mako guda

- Adamu Kwanate mamba a majalisar dokokin jihar Adamawa ya mutu

- Dan majalisan ya yanke jiki ya fadi ne a lokacin kamfen

- Anyi gaggawan daukar Kwanate zuwa asibitin Yola inda anan ya cika

Wani mamba a majalisar dokokin jihar Adamawa, Adamu Kwanate (APC- Nasarawo/Binyeri) ya mutu.

Kamfanin dillancin labaran Najeria (NAN) ta tattaro cewa Kwanate a mutu a ranar Laraba, 6 ga watan Maris kwanaki hudu bayan wani dan majalisa, Abubakar Abdurahman (ADC-Mubi South) ya mutu bayan yayi fama da dogon rashin lafiya.

Kwanate wanda ke neman tazarce a zaben ranar Asabar, 9 ga watan Maris mai zuwa ya yanke jiki ya fadi a lokacin kamfen a mazabarsa sannan aka yi gaggawan kai shi asibitin Yolam inda anan ne ya mutu.

Mohammed Daji, jami’in bayanai na majalisar dokokin jihar wanda ya tabbatar da mutuwar dan majalisar yace: “Yanzun nan na samu mumunan labarin, amma ban rigada na samu cikakken bayanin abunda ya faru ba."

A halin da ake ciki, gaabannin zaben gwamnoni da na yan majalisar jiha, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jawabi ga yan Najeriya inda yayi kira ga su rungumi zaman lafiya a tsarin gudanarwar zaben.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama dilolin kwaya 54 a Kano

A jawabin da yayi a ranar Laraba, 6 ga watan Maris, Shugaban kasar ya bayyana cewa zabe mai zuwa na da matukar muhimmanci duba ga cewa gwaamnoni da yan majalisar jiha sun fi kusa da mutane sosai.

Shugaba Buhari ya mika ta’aziyya ga wadanda suka rasa rayukansu ko suka ji rauni da lokacin ayukan ta’addanci da wasu suka yi yayin zaben Shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel