Ban mutu ba, ina nan da rai da lafiya ta – Matashin da ya yi iyo a kwata saboda Buhari

Ban mutu ba, ina nan da rai da lafiya ta – Matashin da ya yi iyo a kwata saboda Buhari

Aliyu Mohammed Sani, matashin da ake yada jitar-jitar cewar ya mutu bayan ya yi iyo tare da kwankwadar ruwan kwatami a Bauchi, yana nan daram da rai da lafiyar sa.

Da ya ke Magana da wakilin jaridar Daily Trust ta wayar tarho a yau, Laraba, Sani ya ce labarin da ake yada wa a dandalin sada zumunta cewar ya mutu ba gaskiya ba ne.

Sani, mai sana’ar fenti, ya yi watsi da jita-jitar cewar an garzaya da shi asibiti bayan ya kwankwadi ruwan kwatar.

Sani ya ci al washin yin wanka tare da kwankwadar ruwan kwata matukar shugaba Buhari ya sake lashe zabe.

Ban mutu ba, ina nan da rai da lafiya ta – Matashin da ya yi iyo a kwata saboda Buhari
Matashin da ya sha ruwan kwatami saboda Buhari
Asali: UGC

Matashin ya cika alkawarin da ya dauka bayan hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta (INEC) ta sanar da cewar shugaba Buhari ne ya yi nasarar lashe zaben kujerar shugaban kasa da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu. Bayan sani ya cika da alkawarin da ya dauka ne hotunan sa su ka mamaye dandalin sada zumunta.

Amma sai ga shi a jiya, Talata, wasu rahotanni na yawo a gari cewar Sani yam utu bayan ya gamu wa da wata cuta a cikin sa sakamakon ruwan kwatan da ya sha.

DUBA WANNAN: Fara wa da iya wa: Atiku ya samu nasara ta farko a kotun sauraron karar zabe

A yanzu haka maganar da na ke da kai ina kan hanyar koma wa cikin garin Bauchi bayan mun je mun yi aikin fenti a wani wuri da ke da nisa da cikin gari,” a cewar Sani.

A cewar sa, ya sha ruwan kwatami tare da yin iyo a ciki domin cika alkawarin da ya dauka a gaban dumbin jama’a cewar zai yi hakan idan Buhari ya ci zabe.

Da gaske ne na dauki alkawarin yin hakan kafin a yi zabe, na cika alkawarin da na dauka kuma ban a nadamar abin da na aikata,” matashin ya fada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel