Hadimin tsohon Gwamna Fayose ya sauya sheka zuwa APC

Hadimin tsohon Gwamna Fayose ya sauya sheka zuwa APC

Kimanin Mutane 100 na hannun daman tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, a yankin karamar hukumar Ifelodun da kuma Irepodun, sun sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.

Hadimin tsohuwar gwamnatin Fayose akan kula da harkokin kananan hukumomi, Mista Ayodeji Adu, na daya daga cikin na manyan jiga-jigai da suka jagoranci guguwar sauyin sheka daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC.

Tsohon Gwamnan jihar Ekiti; Ayodele Fayose
Tsohon Gwamnan jihar Ekiti; Ayodele Fayose
Asali: Twitter

Mista Adu da sauran jiga-jigan PDP sun bayar da sanawar sauyin sheka yayin taron yakin neman zabe da aka gudanar a yau Laraba cikin yankin Afao Ekiti na dan takarar kujerar majalisar dokoki na jam'iyyar APC, Hakeem Jamiu.

Cikin wakilcin da jagorancin guguwar ta sauyin sheka, hadimin tsohon gwamnan yayin zayyana jawaban sa ya bayyana cewa, sun yanke shawarar sauya sheka daga PDP zuwa APC sakamakon muradin kyawawan akidun jagoranci na gwamnan jihar, Kayode Fayomi.

Da yake ci gaba da bayyana dalilan su, Mista Adu ya ce tsananin kishin kasa gami da hankoron bunkasar ci gaban jihar Ekiti da kuma Najeriya baki daya ya sanya suka sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

KARANTA KUMA: Zaben Gwamna: Kungiyar magoya bayan Buhari ta amince da dan takarar jam'iyyar ADC a jihar Adamawa

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, kungiyar magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari reshen Arewa maso Gabashin Najeriya, ta yi shimfidar goyon baya kan dan takarar kujerar gwamnan jihar Adamawa na jam'iyyar ADC, Abdulaziz Nyako.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel