Kungiyar labaran Buhari ta saki yadda za ta tallafawa dukkanin yan takarar gwamna na APC

Kungiyar labaran Buhari ta saki yadda za ta tallafawa dukkanin yan takarar gwamna na APC

Gabannin zabeen gwamna da na majalisar dokokin jiha wanda za a gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris, kungiyar labaran Buhari wato Buhari New Media Centre (BNMC), wata gidauniya da ta mayar da hankali kan kamfem din Buhari a yanar gizo, ta nuna jajircewa 100 bisa 100 ga nasara a zaben dukkanin gwamnonin jiha ga yan takarar da ke takara a APC.

Da take yada wasu bayanai a shafinta na Facebook a ranar Talata, 5 ga watan Fabrairu, kunciyar ta BNMC ta rubuta: “Wannan shine shawarar da muka yanke kuma za mu tsaya akan haka sannan mu kare shi da manyan yatsunmu a ranar Asabar.”

KU KARANTA KUMA: Yan kwanaki kafin zaben Gwamna: Kansilolin PDP 15 sun sauya sheka zuwa APC a jihar Kwara

A halin da ake ciki, Jam'iyyar APC a yau Talata ta yi karin haske tare da bayyana matsayar ta kan yunkurin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, shigar da kara wajen neman hakkin sa a shari'ance biyo bayan babban zaben kasa.

Kakakin kungiyar yakin neman zaben kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Festus Keyamo, ya bayyana cewa jam'iyyar ba ta da wani nufi na hana Atiku neman hakkin sa a shari'ance biyo bayan babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel