Babu wani shiri da ake na tsige Sultan na Sokoto- APC

Babu wani shiri da ake na tsige Sultan na Sokoto- APC

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Sokoto ta nisanta kanta daga jita-jitan cewa tana shirin tsige Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, idan har ta lashe zaben gwamna.

Shugaban jam’iyyan, Isa Sadiq Acida, ya bayyana hakan ne ga yan jarida jiya a Sokoto.

Yace jam’iyyar adawa ce tayi wannan kulle kullen, ta kuma yi hakan ne domin batanci ga martaban wassu mutanen kirki da aka alakanta ga wannan ikirarin.

"Tabbatacce Sultan ne uba ga dukkan musulmai kuma mun kasance masu rungumar darajojin al’adunmu da addinin mu,” a cewar Acida.

Babu wani shiri da ake na tsige Sultan na Sokoto- APC
Babu wani shiri da ake na tsige Sultan na Sokoto- APC
Asali: UGC

A baya mun ji cewa an shiga cacar baki, nuna ma juna yatsa tare da murza gashin baki tsakanin manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a jahar Sakkwato biyo bayan wasu rade rade dake yawo a farfajiyar siyasar jahar na cewa wata jam’iyya ta dauki alwashin tsige mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar.

KU KARANTA KUMA: Yan kwanaki kafin zaben Gwamna: Kansilolin PDP 15 sun sauya sheka zuwa APC a jihar Kwara

Da fari dai jam’iyyar PDP mai mulki a jahar Sakkwato ce ta fara bayyana damuwarta da shirin da ta yi ikirarin jam’iyyar APC ta kulla na cewa idan har ta samu nasara a zaben gwamnan jahar da zai gudana a ranar 9 ga watan Maris, lallai za ta tsige Sarkin Musulmi, ta nada sabo.

A ranar Litinin, 5 ga watan Maris ne wasu matasa suka shirya tattaki a cikin garin Sakkwato har zuwa fadar mai alfarma sarkin Musulmi, inda suka bayyana makasudin shirya gangamin shine don ankarar da Sarkin game da shirin da APC ke yin a tsigeshi daga kujerarsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel