Boko Haram: ISWAP ta tsige Albarnawi, ta nada sabon shugaba

Boko Haram: ISWAP ta tsige Albarnawi, ta nada sabon shugaba

Kungiyar IS reshen Afrika ta yamma (ISWAP) ta sanar da tsige shugabanta, Abu Mus’ab Albarnawi, a wani sakon sautin murya da kungiyar ta fitar da misalign karfe 06:13 na yammacin yau, Litinin, kamar yadda dan jarida Ahmad Salkida ya wallafa a shafinsa na Tuwita (@A_salkida).

Kazalika, kungiyar ta sanar da nada Abu Abdullahi Ibn Umar Albarnawi a matsayin sabon shugabanta. ISWAP ba ta bayyana dalilin canjin shugabancin ba.

Abu Mus'ab Albarnawi ya zama shugaban ISWAP ne bayan ya kafa tsagin kungiyar Boko Haram, lamarin da ya jawo batawar sa da Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram bayan mutuwar Muhammad Yusuf, shugaban kungiyar na farko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel