Na so ace zan iya gayyatar dukkanin yan Najeriya miliyan 15 da suka zabi Buhari zuwa liyafar cin abinci – Aisha Buhari

Na so ace zan iya gayyatar dukkanin yan Najeriya miliyan 15 da suka zabi Buhari zuwa liyafar cin abinci – Aisha Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren ranar Asabar da ya gabata ya yi bayanin cewa Najeriya ta dauki lokaci kafin ta gyaru saboda tsawon lokacin da tsohuwar gwamnatin Peoples Democratic Party ta bata tana mulki na tsawon shekaru 16.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da uwargidan Shugaban kasar Aisha Buhari ta ba mata da matasa tabbacin samun gurbi gwamnatin Buhariu na biyu, cewa Shugaban kasar zai dinke barakar da ke tsakanin masu kudi da talaka.

Na so ace zan iya gayyatar dukkanin yan Najeriya miliyan 15 da suka zabi Buhari zuwa liyafar cin abinci – Aisha Buhari
Na so ace zan iya gayyatar dukkanin yan Najeriya miliyan 15 da suka zabi Buhari zuwa liyafar cin abinci – Aisha Buhari
Asali: Twitter

Da yake jawabi a wani liyafar cin abinci da kungiyar mata da matasa suka shirya a fadar Shugaban kasa, Buhari wanda ya sha alwashin kin bijirewa yardar da yan Najeriya suka bashi a zaben da ya gabata, yace nasararsa alama ce da ke nuni ga cewar yan Najeriya sun aminta da chanjin da gwamnatinsa ke kai.

Daga nan sai yayi alkawarin amfani da shekaru hudu da yake da su anan gaba wajen kamala abubuwan da ya fara.

KU KARANTA KUMA: Idan akwai ‘Yan takaran da su ka fi ‘Yan Jam’iyyar APC kyau, ku zabe su – Inji Buhari

A nata jawabin daga hannun daraktan labaranta, Suleiman Haruna, Aisha Buhari tace Shugaban kasar na sane da rawar ganin da mata da matasa suka taka a lokacin kamfen dinsa da kuma zabensa, inda tayi alkawarin cewa za a dama dasu a gwamnatinsa na biyu.

Tace: “Na so ace zan iya gayyatar dukkanin yan Najeriya miliyan 15 da suka zabi Shugaban kasa zuwa wajen wannan liyafar cin abincin, amma wajen ba zai karbi dukkaninku ba. Don haka bari na yi godiya gare ku sannan na baku tabbacin cewa kun yi zabi nagari.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel