Manyan jiragen dankaro guda 15 sun shigo Najeriya dauke da man fetir

Manyan jiragen dankaro guda 15 sun shigo Najeriya dauke da man fetir

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya, NPA, ta bayyana cewar akalla manyan jiragen ruwa guda goma sha biyar ne suke sauke man fetir da dangoginsa a tashar jiragen ruwa na tsibirin Tin Can da na Apapa na jahar Legas.

Legit.ng ta ruwaito hukumar NPA ta sanar da haka ne cikin sanarwar data fitar a ranar Juma’a, 1 ga watan Maris, inda tace a jirage biyu sun sauke tataccen man fetir da man dizil a ranar Juma’ar.

KU KARANTA: Masu amfani da yanar gizo a Najeriya sun kai miliyan 113.8 - NCC

Manyan jiragen dankaro guda 15 sun shigo Najeriya dauke da man fetir
Jirgin dankaro
Asali: UGC

Sanarwar ta kara da cewa sauran jiragen guda goma sha biyu sun dauko dakon kayayyaki da suka hada a Fulawa, siga, sundukai, kalanzir da sauran hajojin yan kasuwannin Najeriya da suka yo oda daga kasashen waje.

Idan za’a tuna, mun kawo muku rahoto cewa a jiya Alhamis ma wasu manya manyan jiragen dankaro na cikin ruwa guda goma sha uku sun fara sauke kayan da suka dauko daga sassan duniya suka shigo dasu Najeriya a tashoshin jiragen ruwan Najeriya dake jahar Legas.

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya, NPA ce ta bayyana haka cikin sanarwar da take fitarwa a kullu yaumin, inda tace jiragen goma sha uku suna sauke kayan nasu ne a tashar Apapa da tashar tsibirin Tincan.

Hukumar NPA ta bayyana cewa daga cikin jiragen akwai guda daya dake dauke da man dizil, kuma ya fara sauke man ne da sanyin safiyar Laraba, 27 ga watan Feburairu, kamar yadda hukumar ta tabbatar.

Sauran abubuwan da jiragen sauran jirage goma sha biyu suka dauko sun hada da man fetir, pulawa, sundukai, siga, man jiragen sama, da kuma sauran hajojin yan kasuwan Najeriya daban daban da suka yo odansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel