Jami’ai sun tashi dandalin shan wiwi 45, tare da cafke mashaya 250 a Kano

Jami’ai sun tashi dandalin shan wiwi 45, tare da cafke mashaya 250 a Kano

Jami’an hukumar yaki da fatauci, sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi, NDLEA, sun tabbatar da kama mashaya da dillalan wiwi da sauran kayayyakin maye guda dari biyu da hamsin (250) a wasu samame daban daban da suka kai a jahar Kano.

Kwamandan NDLEA, Ibrahim Abdul ne ya bayyana haka ga manema labaru a ranar Alhamis, 28 ga watan Feburairu, yayin da yake bayani game da ayyukan hukumar a jahar Kano, inda yace yawancin mutanen da suka kama suna dauke da miyagun kwayoyi ne.

KU KARANTA: Hajiya mai waina ta rabar da wainarta duka albarkacin nasarar Buhari

Legit.ng ta ruwaito kwamandan na bugun kirki yana cewa sakamakon jajircewa da hukumar NDLEA ke nunawa a jahar Kano yasa matasa sun rage ta’ammali da haramtattun kwayoyi irinsu Tramadol da Codeine.

Haka zalika yace hukumar ta kama kilo 1,637 na kwayoyi daban daban da kayan maye, daga cikin kilo dari takwas da saba’in da biyu (872) na tabar wiwi, giram 400 na hodar iblis, kilo 718 na wasu sinadarai masu sanya maye da kuma giram 50 na kwayar Khat.

Bugu da kari kwamanda Abdul yayi kira ga yan siyasa dasu kauce ma amfani da matasa wajen bangan siyasa, tare da basu miyagun kwayoyi da zai kawai da hankulansu ta yadda zasu iya aikata aika aika a wannan lokaci.

A yanzu haka hukumar ta kaddamar da bincike akan wasu yan siyasan Kano da ta gayyata wadanda a gidajensu ta kama wasu daga cikin matasa yan kwayan da suke hannunta a yanzu, sa’annan yayi kira ga jama’a dasu kasance masu bin doka da oda.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel