Matashiyar da ta shiga jami’a a shekara 15 sannan ta kammala a shakara 18 ta sanarda labarinta

Matashiyar da ta shiga jami’a a shekara 15 sannan ta kammala a shakara 18 ta sanarda labarinta

Ba sabon labari bane cewa yan Najeriya na da baiwa da tarin kokari. Matasan Najeriya sun kasace masu fasaha inda suke nuna kwazo da kokarinsu domin inganta kasar, don haka wannan matashiyar ta sanar da labarin yadda tayi nata bajintar.

Wata matashiyar yarinya ta je shafinta na zumunta domin wallafa dukkanin nasarorin da ta samu. Matashiyar mai suna Maryam Jallo ta sanar da tarin nasararotin rayuwarta a shafin twitter.

Matashiyar ta bayyana yadda ta yi nasarar lashe jarrbawar JAMB tana da shekara 15. Ta sanar da cewa ta bar Najeriya domin ci gaba da karatunta a wani jami’a da ke kasar waje.

Matashiyar da ta shiga jami’a a shekara 15 sannan ta kammala a shakara 18 ta sanarda labarinta
Matashiyar da ta shiga jami’a a shekara 15 sannan ta kammala a shakara 18 ta sanarda labarinta
Asali: Twitter

Jallo tayi bayanin cewa ta samu dammar karanta fannoni biyu. Matashiyar ta bayyana cewa ta kammala karatun digiri tana da shekara 18.

KU KARANTA KUMA: Kalli yadda Aisha Buhari ta taka rawa bayan mijinta ya lashe zabe (bidiyo)

A yayinda ta cika shekara 21 matashiyar ta zamo cikakkiyar likita sannan kuma mammalakiyar wani kamfani mai zaman kansa a shekara 22.

Matashiyar ta kuma bayyana cewa bayan kafa kamfani mai zaman kansa, kamfanin ya kammala kasa-kasai 48.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel