PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben Shugaban kasa na jihar Katsina

PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben Shugaban kasa na jihar Katsina

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta ki amincewa da sakamakon zaben Shugaban kasa daga jihar Katsina kan zargin rashin bin ka’ida.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma dan asalin jihar ya samu kuri’u 1,232,133 inda ya kayar da Atiku wanda ya samu kuri’u 303,056.

Salisu Majigiri, Shugaban PDP a jihar ya bayyana matsayar jam’iyyar a wani taron manema labarai a ranar Talata a Katsina.

PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben Shugaban kasa na jihar Katsina
PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben Shugaban kasa na jihar Katsina
Asali: UGC

Ya yi zargin cewa akwai wasu magu-magun zabe a wasu kananan hukumomi na jihar a lokacin zabe don haka PDP bata yarda ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Saraki zai tuna cewa akwai Allah – Ndume yayi murnar faduwar Shugaban majalisar dattawa

A wani lamari makamancin wannan mun samu labari cewa APC mai mulki ta nuna rashin amincewar ta da sakamakon zaben shugaban kasa da ya fito daga jihar Akwa-Ibom.

Wani wanda ya wakilci APC wajen kididdigar kuri’u yace akwai babbar matsala da zaben. Wakilin jam’iyyar APC a zaben na 2019, Samuel Akpan, ya fadawa ‘yan jarida cewa ba za su amince da sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a jihar Akwa-Ibom. Wakilin na APC ya nemi INEC ta sake zabe a daukacin Jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel