Sakamakon zabe: Buhari ya yi wa Atiku raga-raga a jihar Yobe

Sakamakon zabe: Buhari ya yi wa Atiku raga-raga a jihar Yobe

Sakamakon zabe da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta sanar a matakin kujerar shugaban kasa ya nuna cewar jam’iyyar APC mai mulki ta samu kuri’u 497,914 yayin da jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 50,763 kacal a zaben da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Baturen zaben kujerar shugaban kasa a jihar Yobe, Farfesa Abubakar Gundiri, ne ya sanar da sakamakon da aka kammala tattara wa daga kananan hukumomi 17 da jihar ke da su. Ya sanar da sakamakon zaben ne yau, Lahadi, a gidan gwamatin Yobe da ke Damaturu, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewar jihar Yobe na adadin ma su kada kuri’a 1,365,913, wanda daga cikin su aka tantance adadin mutane 601,059 da su ka yi zabe a ranar Asabar.

Sakamakon zabe: Buhari ya yi wa Atiku raga-raga a jihar Yobe
Cibiyar tattara sakamakon zabe ta kasa
Asali: UGC

A cewar baturen zaben, an samu jimillar kuri’u ingantattu 559,365, yayin da aka samu kuri’u 26,772 da su ka lalace.

Farfesa Gundiri ya ce an kada jimillar kuri’u 586,137, wanda daga ciki jamm’iyyar APC ta samu kuri’u 497,914, yayin da jam’iyyar PDP ta samu adadin kuri’u, 50,763.

DUBA WANNAN: Sakamakon zabe: Buhari ya yi wa Atiku raga-raga a jihar Yobe

Ya yaba wa ma su zabe, ma su ruwa da tsaki da wakilan jam’iyyu bisa hadin kan da su ka bayar wajen ganin an gudanar da zabe cikin lwanciyar hankali da lumana a jihar.

Kazalika, wakilan jam’iyyun APC, Dakta Zaji Bunu, da na PDP, Dakta Abdu Bulama, sun amince da sakamakon zabe kuma sun rattaba hannu a kan takardar sakamakon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel