Cikakken sakamako: Buhari ya kai PDP kasa a jihar Legas
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe zaben kujerar shugaban kasa a jihar Legas, ya kayar da abokin takarar sa, Atiku Abubakar, na jam’iyyar PDP da banbancin kuri’u 132,798.
Banbancin kuri’un da ke tsakanin Buhari da Atiku ya gaza banbancin kuri’u 160,143 da Buhari ya kayar da Jonatahan da su a zaben shekarar 2015, Buhari ya samu kuri’u 792, yayin da Jonatahan ya samu kuri’u 632,327.
A sakamakon da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta sanar a cibiyar tattara sakamo ta jihar Legas da ke Yaba a yammacin yau, Litinin, Buhari ya samu kuri’u 580,814, yayin da Atiku ya samu kuri’u 448,016.
Buhari ya samu nasara a kananan hukumomi 15 daga cikin 20 da ke jihar Legas, Atiku ya samu nasara a kananan hukumomi biyar da ‘yan kabilar Igbo ke da rinjayen jama’a.
Jihar Legas na da kananan hukumomi 20 kuma yanzu haka INEC ta sanar da sakamakon zabe a kananan hukumomi 16.
Kafin samun wannan cikakken sakamako, Legit.ng ta kawo ma ku labarin cewar shugaban kasa Muhammadu na jam’iyyar APC ne ke kan gaba yanzu haka daga sakamakon zaben kananan hukumomi 15 da hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta sanar yayin da sakamako ke cigaba da shigowa cibiyar tattara sakamako ta jihar da ke Yaba.
A sakamakon da aka sanar zuwa yanzu, Buhari ya lashe zabe a kananan hukumomi 12 yayin da abokin hammayyar sa, Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP ya samu nasara a kananan hukumomi uku.
Ana dakon sakamako daga kananan hukumomi biyar yayin da ake wallafa wannan rahoto.
DUBA WANNAN: Sakamakon zabe: Atiku ya kayar da Buhari a jihar Ondo
Ga sakamakon kananan hukumomin da aka bayyana;
1. Apapa
APC – 18,170
PDP – 11,295
2. Ikorodu
APC: 40,719
PDP: 21,252
3. Ibeju/Lekki
APC: 12,179
PDP: 9,222
4. Lagos lsland
APC: 27,452
PDP: 7,396
5. Epe
APC: 17,710
PDP: 13,305
6. Ikeja
APC: 23,638
PDP: 21,518
7. Badagry
APC: 21,417
PDP: 17,936
8. Agege
PDP: 16,497
APC: 36,443
9. Eti-Osa
PDP: 25,216
APC: 20,963
10. Ifako/Ijaiye
APC: 33,419
PDP: 18,100
11. Mushin
PDP: 20,277
APC: 43,543
12. Oshodi/lsolo
PDP: 28,806
APC: 29,860
13. Lagos Mainland
PDP: 15,137
APC: 22,684
14. Ojo
PDP: 29,019
APC: 24,333
15. Surulere
APC: 30,621
PDP: 31,603
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng