Sakamako: Ina da yakinin zan lashe zabe – Atiku

Sakamako: Ina da yakinin zan lashe zabe – Atiku

Atiku, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya yi kira ga shugaba Buhari da ya tsawatar wa jiga-jigan ‘yan jam’iyyar APC domin ganin ba su kawo rudani a cibiyoyin tattara sakamakon zaben ba.

A wani jawabi da mai taimaka ma sa a bangaren yada labarai, Mista Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya yi godiya ga ‘yan Najeriya bisa yadda su ka yi tururuwa wajen fito wa domin kada ma sa kuri’a a zaben da aka yi jiya, Asabar, 23 ga watan Fabarairu.

Ina mika godiya ga miliyoyin ‘yan Najeriya bisa yadda su ka yi tururuwar fito wa domin kada min da jam’iyya ta kuri’un su, ba tare da sun daga zaben da aka yi ya kasha ma su jiki ba.

“Kuri’u ma fi rinjaye da za mu samu daga yankin kudu maso gabas, kudu maso kudu da karin adadin kuri’un da za mu samu daga kudu maso yamma da arewa ta tsakiya, mu na da tabbacin cewar PDP za ta samu nasara.

Sakamako: Ina da yakinin zan lashe zabe – Atiku
Atiku yayin kada kuri'a mazabar sa
Asali: UGC

“Mu na sa ran sanar da ku labara mai dadi daga ragowar sassan Najeriya nan ba da dadewa ba.

DUBA WANNAN: Sakamako: Duk da an sake kirga kuri’u, Atiku ya lallasa Buhari a fadar shugaban kasa

“Mu na kiira da jama’ar Najeriya d su kwantar da hankalim su domin kwanan nan za su yi bankwana da wahalar da su ka shafe hekaru hudu su na sha,” a cewar Atiku.

Atiku ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kara sa-ido a cikin sa’o’i 48 domin kare kuri’un su da su kada a akwatinan sun a zabe tare da yin zargin cewar jam’iyyar APC na kokarin shirya magudi a cibiyoyin tattara sakamako.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel