Yan bindiga sun tashi kauyuka 17, sun kashe 5, sun yi garkuwa da 35 a jahar Neja

Yan bindiga sun tashi kauyuka 17, sun kashe 5, sun yi garkuwa da 35 a jahar Neja

Gungun yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai wasu muggan samame a wasu kauyuka goma sha bakwai, 17, dake cikin kananan hukumomin Rafi da Shiroro na jahar Neja, inda suka kashe akalla mutane biyar a hare haren duka.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito baya da haka yan bindigan sun yi awon gaba da mutane Talatin da biyar, 35, kamar yadda hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Neja, NSEMA ta tabbatar a ranar Litinin, 18 ga watan Feburairu.

KU KARANTA: Ku kawo min dauki, Gwamna na neman kassara ni – Inji Mataimakin Gwamnan jahar Kogi

Kaakakin NSEMA, Ibrahim Audu ya bayyana cewa hare haren sun wakana ne a daren Alhamis din data gabata, a dalilin haka mutane dubu uku da dari biyar suka rasa matsuguninsu, inda a yanzu suke gudun hijira a makarantar Firamari ta Kagara da Firamarin Pandogari.

Hukumar tace gwamnatin jahar ta samar da kayayyakin jin kai ga jama’an da harin ya shafa, da suka hada da kayan abinci, katifu da bargo, sa’annan ya kara da cewa hukumar zata fara raba kayan cikin makonnan.

“Mun samar da dakunan wucin gadi ga yan gudun hijiran a sansanonin, haka zalika mun fara daukan bayanan jama’an dake sansanonin, kuma hukumar NSEMA ta tura jami’an kiwon lafiya don kulawa dasu, bugu da kari gwamnatin jahar ta umarci mu samar da duk abinda ake bukata a sansanonin.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindiga sun halaka mutane uku da basu ji ba, basu gani ba, tare da wani jami’in rundunar Sojan kasan Najeriya, a yayin wani hari da suka kai kauyen Kasai dake cikin karamar hukumar Batsari ta jahar Katsina.

Wannan lamari ya faru ne da misalin karfe daya na daren Lahadi, inda yan bindigan suka jikkata mutane da dama a kauyen, sa’annan suka kora sama da shanu dari biyu. Sai dai rahotanni sun bayyana jama’an kauyen suka tari yan bindigan inda aka yi ta bata kashi, amma daga bisani suka fi karfin jama’an kauyen, daga baya kuma Sojoji suka isa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: