Lamari ya lalace: Amarya yar shekara 19 ta halaka mijinta da wuka

Lamari ya lalace: Amarya yar shekara 19 ta halaka mijinta da wuka

Wata mata mai shekaru goma sha tara, 19 a Duniya, Mary Adeniyi ta bayyana gaskiyar dalilin da yasa ta kashe mijinta, wanda ta caccaka ma wuka a jikinsa har sai daya fadi matacce, inda tace ta dauki wannan mataki ne saboda yana zarginta da cin amana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mary ta bayyana haka ne rundunar Yansandan jahar Legas, kamar yadda kaakakin rundunar, Chike Oti ya bayyana, inda yace Mary ta shaida musu cewa Mijinta ya dade yaa zarginta da bin maza, kuma bata jin dadin hakan.

KU KARANTA: Aiki na kyau: Wasu gungun gagga gaggan yan fashi da makami sun fada komar Yansanda

Lamari ya lalace: Amarya yar shekara 19 ta halaka mijinta da wuka
Uwargida Mary
Source: UGC

“Mijinta ya dade yana zarginta da neman maza, kuma ita bata jin dadin wannan zargi nasa, don haka rikici ya barke a tsakaninsu a ranar Juma’a bayan ya sake zarginta da kwana da wani saurayinta, ana cikin haka ne ta dauki wuka ta luma masa a wuya, nan take ya fadi matacce.” Inji Dansanda Oti.

Ita ma Mary, wanda take zama a unguwar Shagamu dake garin Ikoyin jahar Legas ta tabbatar da wannan labari, inda tace ta kashe Mijinta ne sakamakon bacin ran da ta samu kanta a ciki, sai dai a yanzu ta bayyana nadamarta game da kisan.

“Ni fa ban san lokacin da na dauki wuka na caka masa a wuya ba, gaskiya banyi nufin kasheshi ba, nayi nadamar abinda na aikata, kuma ina neman gafara.” Inji Mary, Amarya mai shekaru goma sha tara da haihuwa.

A wani labarin kuma wani jami’in hukumar yaki da fasa kauri ta kasa, watau kwastam ya dirka ma wani mutumi bindiga wanda yayi sanadiyyar mutuwarsa har lahira, a ranar Lahadi a garin Ijebu Ode na jahar Ogun.

Wannan kisa ya faru ne a gaban jama’a kamar yadda wani bidiyo dake yawo a kafafen sadarwar zamani ya nuna, inda aka hangi wata mata tana ihu hannunta a kai sakamakon tashin hankalin da ta shiga ganin yadda kwastam din ya kashe mutumin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel