Rikicin Kaduna: Sakamakon kashe mutane 66, al'ummar Fulani sun yi kaura daga muhallansu

Rikicin Kaduna: Sakamakon kashe mutane 66, al'ummar Fulani sun yi kaura daga muhallansu

Rahotannin da muke samu na nuni da cewa al'ummar Fulani da ke zaune a garuruwan karamar hukumar Kajuru, jihar Kaduna, sun bar garuruwan nasu, tare da yin hijira zuwa wasu garuruwan domin samun mafaka, bayan da aka kai masu wani hari a ranar 11 ga watan Fabreru, inda har mutane 66 suka mutu, wadanda mafi yawansu mata da kananan yara ne suka mutu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa an kona gidaje, dabbobi, ababen hawa, kayan dakin dafa abinci, ya yin da aka haka rami guda daya aka binne gawarwakin mata da kananan yara.

Gwamna Nasiru El-Rufai, wanda ya samu rakiar babban ofisan da ke jagorantar rundunar soji ta daya, kwamishinan 'yan sanda da kuma 'yan jaridu, ya ziyarci kauyukan da lamarin ya faru a ranar Asabar, inda bai samu mutun ko daya a cikinsu ba.

KARANTA WANNAN: Bar murna karenka ya kama kura - Atiku ya caccaki Buhari kan dage zabe

Rikicin Kaduna: Sakamakon kashe mutane 66, al'ummar Fulani sun yi kaura daga muhallansu

Rikicin Kaduna: Sakamakon kashe mutane 66, al'ummar Fulani sun yi kaura daga muhallansu
Source: Facebook

Da ya ke jawabi, babban kwamandan rundunar sojin, Manjo-Janar Faruk Yahaya ya ce an tura dakarun soji garuruwan da lamarin ya shafa, tare da taimakon wasu mazauna kauyukan, inda suka gano gawarwakin mata da kananan yara guda 37, da aka binne su a cikin rami daya, yayin da kusan kowanne gida an kona shi.

"Zuwa yanzu mun samu adadin mutane 66 da suka mutu, ta hanyar hadin guiwa da sauran hukumomin tsaro, zamu tabbata mun wanzar da zaman lafiya tare da maido da jama'a zuwa garuruwansu."

A nashi bangaren kwamishinan 'yan sanda, Ahmad AbdurRahman ya bayyana cewa duk da cewa 'yan sanda sun mamaye yankin, hakan bai hana al'ummar garin ficewa daga gidajensu ba, cikin jin tsoron sake kai masu wani harin.

Ya tabbatar da cewa rundunar ta cafke mutane bakwai da ake zarginsu da sa hannu a kai harin, yana mai cewa da zaran an kammala bincike akansu, za a gurfanar da su gaban kotu a ranar Litinin.

Shi ma da ya ke jawabi, gwamnan jihar ya koka kan yadda ake yunkurin cusa siyasa a cikin wannan rikicin tare da kokarin lullube gaskiyar abubuwan da ke faruwa a kasa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel