2019: Atiku zai ci zabe da kaso 56.5% na kuri'un al'ummar Najeriya - Business Day

2019: Atiku zai ci zabe da kaso 56.5% na kuri'un al'ummar Najeriya - Business Day

A yayin da a gobe Asabar, 16, ga watan Fabrairu, al'ummar Najeriya za su yi tururuwa domin kada kuri'ar su wajen zaben kujerar shugaban kasa da kuma 'yan majalisun dokokin na tarayya, ana ci gaba da hasashe dangane da yadda sakamakon zaben zai kasance.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, babban kamfanin jaridar nan na Business Day mai tushe a jihar Legas, ya gudanar da bincike tare kiyasta yadda sakamakon zaben zai kasance tsakanin manyan 'yan takarar biyu masu neman kujerar shugaban kasa.

2019: Atiku zai ci zabe da kaso 56.5% na kuri'un al'ummar Najeriya - Business Day
2019: Atiku zai ci zabe da kaso 56.5% na kuri'un al'ummar Najeriya - Business Day
Asali: UGC

Ko shakka ba bu, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari, da kuma dan takara na jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, sun kasance manya kuma mafi shahara cikin 'yan takara 72 da ke hankoron babbar kujerar jagorancin kasar nan a zaben gobe.

Duba da nazari da kuma binciken da jaridar Business Day ta gudanar, ta yi kiyasi na cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa da ya kasance dan takara na jam'iyyar PDP, zai lashe babban zaben matukar zai tsarkaka daga duk wani nau'i na magudi ko rashin gaskiya.

Cikin kididdigar da babban kamfanin jaridar ya gudanar, alkaluma na tarihi sun tabbatar da cewa, ana samun masu kada kuri'a kimanin kaso 46.6 cikin 100 na adadin masu rajistar zabe zabukan da suka gudana cikin kasar nan a lokutan baya.

KARANTA KUMA: 2019: Rundunar Sojin Sama ta sake tanadar wasu Jirage na jigilar kayayyakin zabe

Baya ga adadin al'ummar kasar nan kimanin miliyan 84 ma su rajistar zabe, kiyasi na jaridar Business Day ya tabbatar da cewa, ana sa ran kimanin kaso 43.65 cikin 100 za su fito domin dangwala kur'in su a yayin zaben na gobe Asabar.

Kididdigar jaridar Business Day da ta jinginawa Atiku nasara matukar zaben zai tsarkaka da gaskiya, ta yi kiyasi na adadin kuri'u da kowanen su zai samu tsakanin sa da shugaba Buhari cikin yakuna shida da ke fadin kasar nan kamar haka:

Arewa ta Tsakiya

Atiku: 2,383,844

Buhari: 2,198,719

Arewa maso Gabas

Buhari: 3,228,738

Atiku: 2,856,191

Arewa maso Yamma

Buhari: 5,543,478

Atiku: 4,434,782

Kudu maso Yamma

Buhari: 2,708,580

Atiku: 2,280,910

Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu

Atiku: Fiye da kuri'u miliyan goma

Buhari: Fiye da kuri'u miliyan biyu

Kiyasin jaridar ya bayyana cewa, Atiku zai yi nasara da kimanin kaso 56.5%, yayin da shugaba Buhari zai samu kaso 40.2% na adadin kuri'u da ake hasashen al'ummar kasar nan za su kada cikin yakunan ta shida.

Kazalika kiyasin ya yi hasashen cewa, sauran 'yan takara da ba za su yi tasiri ba a zaben sakamakon yadda mashahuranci ya takaita kadai a yankin Kudu maso Yamma irin su Kingsley Muoghalu, Omoyele Sowore da kuma Fela Durotaye, za su samu kaso 3.3% na adadin kuri'un al'ummar su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel