Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya Babachir Lawal ya iso Kotu domin gurfana

Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya Babachir Lawal ya iso Kotu domin gurfana

Mun samu cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya isa babbar kotun tarayya da ke garin Abuja domin gurfana gaban kuliya sakamakon takaddamar kan zargin sa da aikata laifuka na zamba da rashawa.

Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya Babachir Lawal ya iso Kotu domin gurfana

Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya Babachir Lawal ya iso Kotu domin gurfana
Source: Depositphotos

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, tsohon babban jami'in gwamnatin ya iso harabar kotun cikin tawaga ta 'yan rakiyar sa da suka kasance jami'an hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a jiya Litinin hukumar EFCC ta cikwikwiye tsohon sakataren gwamnatin inda a yau Talata zai gurfanar gaban kotun tarayya da ke zamanta a garin Maitama bisa jagorancin Alkali Jude Okeke.

KARANTA KUMA: Sauya fasalin kasa zan fara aiwatar wa idan na hau Kujerar mulki - Atiku

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito sun bayyana cewa, tsohon lauyan kolu kuma tsohon Ministan Shari'a na Najeriya, Cif Akin Olujinmi, na daya daga cikin masu wakilcin tsohon sakataren gwamnatin a gaban Kotu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel