Kanal Sagir Musa ya zama sabon Kaakakin rundunar Sojan kasa

Kanal Sagir Musa ya zama sabon Kaakakin rundunar Sojan kasa

Ga duk wanda ya bibiye yaki da Boko Haram da rundunar Sojan kasa ta kaddamar da farko farkon bayyana kungiyar, ba zai rasa sanin kaakakin rundunar dake yaki da yan ta’adda, Laftanal kanal Sagir Musa ba, a yanzu dai shine sabon kaakakin rundunar Sojan kasa gaba daya.

Legit.ng ta ruwaito babban shelkewatar rundunar ce ta sanar da nadin Kanal Sagir Musa a matsayin sabon kaakakinta a ranar Litinin, 11 ga watan Feburairu, wanda kafin nadin nasa shine kaakakin runduna ta 82 dake jibge a jahar Enugu.

KU KARANTA: Dandalin Kannywood; Sanata Kwankwaso ya damka ma Adam Zango darikar Kwankwasiyya

Kanal Sagir Musa ya zama sabon Kaakakin rundunar Sojan kasa

Kanal Sagir Musa
Source: UGC

Wannan nadi na Sagir Musa ya biyo bayan murabus na kashin kai da Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka ya yi ne a Alhamis din data gabata, 7 ga watan Feburairu, wanda hakan ya samar da bukatan maye gurbinsa da wanda ya cancanta.

Sai dai ba Sagir kadai bane ya samu sauyin wajen aiki, akwai manyan hafsoshin Soji da dama da babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ta sauya ma wajen aiki, daga cikinsu akwai.

Kanal A.A Yusuf tsohon babban mai tsaron sashin watsa labaru na rundunar, da aka mayar da shi mataimakin kaakakin runduna ta 82 dake Enugu. Kanal A.D Isa sabon mataimakin daraktan watsa labaru na Operation Lafiya Dole.

Kanal Onyeama Chukwu, sabon mukaddashin daraktam tattara bayanai a shelkwatar tsaro ta kasa. An dauke Birgefiya M.A Masanawa daga shelkwatar rundunar Sojan kasa zuwa Kwamandan ACADA, sai kuma Birgediya H.G Tafida da aka mayar dashi zuwa Daraktan kula wa sufurin Sojoji.

Shima Kanal S Adam ya samu karin girma zuwa mukamin kwamandan sashin kiwon lafiya na rundunar, Birgediya B.A Ilori ya koma mataimakin daraktan sayen kayayyakin aikin rundunar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel