Batan-baka-tan-tan: Kungiyoyi 145 sun bar tafiyar Atiku zuwa tafiyar tazarcen Buhari

Batan-baka-tan-tan: Kungiyoyi 145 sun bar tafiyar Atiku zuwa tafiyar tazarcen Buhari

Yayin da babban zabe na gama gani a najeriya da za'a gudanar a ranar 16 ga watan Fabreru ke kara karatowa, wasu kungiyi akalla 145 dake goyon bayan dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar sun juya masa baya.

Kamar dai yadda muka samu, kungiyoyin dukkan su sun yi wanka ne sannan kuma suka shelanta komar su jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) tare da dan takarar shugabancin kasar ta Shugaba Muhammadu Buhari.

Batan-baka-tan-tan: Kungiyoyi 145 sun bar tafiyar Atiku zuwa tafiyar tazarcen Buhari

Batan-baka-tan-tan: Kungiyoyi 145 sun bar tafiyar Atiku zuwa tafiyar tazarcen Buhari
Source: Twitter

KU KARANTA: Matashi yayi barazanar kashe kan sa idan Atiku ya ci zabe

Legit.ng Hausa ta samu cewa wasu daga cikin kungiyoyin da suka koma APC din daga PDP sun hada da Atiku Reloaded, Atiku Support Group, Unique Women for Atiku, Dynamic Women for Atiku, da kuma United Group for Atiku.

Sauran kuma sun da Grassroots Initiative for Atiku da kuma Edo Ambassadors for Atiku da dai sauran su.

Kungiyoyin haka zalika kamar yadda muka samu sun samu kyakkyawar tarba ne zuwa APC a wurin wani kayataccen bikin murna da aka shirya masu a garin Abuja da ya samu halartar wasu jiga-jigan jam'iyyar ta APC.

Wadanda suka halarci bikin karbar tasu dai sun hada da mambobin kwamitocin kamfen din yakin neman zaben na shugaba Buhari da Alhaji Buba Marwa da tsohon Insifectan yan sandan Najeriya Suleiman Abba da dai sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel