Zan aske gashin kaina idan Buhari ya ci zabe – Bello Muhammad Bello

Zan aske gashin kaina idan Buhari ya ci zabe – Bello Muhammad Bello

- Jarumin wasan Hausa Bello Muhammad Bello da aka fi sani da BMB ya sa alwashin aske sumar da ke kansa muddin aka sanar cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ci zabe

- Bello yace har kudi an saka masa don ya aske sumarsa amma ya ki askewa

- Yace amma zai aske sumar saboda murnar nasarar cin zaben Buhari

Shahararen jarumin nan na Kannywood, Bello Muhammad Bello da aka fi sani da BMB ya sa alwashin aske sumar da ke kansa muddin aka sanar cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ci zaben ranar 16 ga watan Fabrairu, 2019.

Jarumin ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke hira da gidan jaridar Daily Trust, inda ya ce, har kudi an saka masa don ya aske sumarsa amma ya ki askewa, amma zai aske sumar saboda murnar nasarar cin zaben Buhari.

Zan aske gashin kaina idan Buhari ya ci zabe – Bello Muhammad Bello
Zan aske gashin kaina idan Buhari ya ci zabe – Bello Muhammad Bello
Asali: Twitter

Bello, wanda darakta ne kuma marubucin labaran fim ya ce sumar da ke kansa ta kai shekaru sama da goma yana yawo da abinsa, kuma har wani furodusa ya yi min tayin Naira miliayan daya da rabi na aske na fito a fim dinsa amma na ki. Amma yanzu na yi alwashin zan aske don murnar nasarar shugaba Buhari.

KU KARANTA KUMA: Baki-ke-yanka-wuya: Wani jigon PDP a Kaduna ya furta kalaman da suka jefa shi a tsomomuwa

A wani lamari na daban, mun ji cewa wani dan majalisar dokoki na jihar Bauchi, Aminu Tukur, ya sha alwashin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zai samu kaso 50 na kuri’u ba a jihar Bauchi a zaben Shugaban kasar da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Tukur ya bayyana cewa Buhari ba zai samu irin goyon bayan da ya samu ba a baya daga jihar saboda goyon bayan Gwamna Mohammed Abubabakar da yayi a matsayin dan takarar gwamnan jihar na APC a zabe mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

/

Asali: Legit.ng

Online view pixel