Hotuna da Bidiyo: Jihar Taraba ta cika ta banbatse domin Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya dira filin kwallon Jolly Nyame da ke garin Jalingo, babban birnin jihar Taraba a ranan Alhamis, 7 ga watan Febrairu, 2019 domin yakin neman zabensa na karo biyu da za'a gudanar nan da kwanaki 9.
Shugaban kasan ya cigaba da yakin neman zabensa ne a yau bayan kammala taron yankin Yarbawa da Inyamurai face jihar Legas.
Bayan kammala taro a Taraba, shugaba Buhari zai garzaya mahaifar Alhaji Atiku Abubakar, jihar Adamawa, domin kamfe.
Ranan Asabar, zai garzaya babban birnin jihar Legas domin cigaba da gabatar da sakon Nexl Level. Jihar Legas ta kasance babbar jihar da jam'iyyar APC tafi yawan mabiya a yankin kudu maso yamma, da akafi sani da yankin Yarbawa.
Ana sa ran cewa duk da karshen mako ne, zuwan Buhari zai jawo cikas wajen sufuri musamman a kwaryar birnin Legas.
Gabanin halartan taron yakin neman zaben, shugaban kasan zai kai ziyarar wurare daban-daban musamman fadar sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, domin gaisuwar ban girma.

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
KU KARANTA: Atiku da Obasanjo na da hannu cikin kashe tsohon ministan sharia - Soyinka
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng