Atiku ba dan Najeriya ba ne, shine ya kayar da Ekwueme zabe a 1999 - Nnamdi Kanu

Atiku ba dan Najeriya ba ne, shine ya kayar da Ekwueme zabe a 1999 - Nnamdi Kanu

- Shugaban kungiyar ‘yan aware ta Biyafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya ce Atiku Abubakar dan asalin kasar Kamaru ne

- Shugaban na IPOB ya zargi Atiku da jawo faduwar Alex Ekwueme a takarar kujerar shugaban kasa da ya yi a shekarar 1999

- Kazalika, Kanu ya bayyana cewar ya gudu ya bar Najeriya ne a shekarar 2017 saboda sojoji na yunkurin hallaka shi

Shugaban kungiyar ‘yan aware ta Biyafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya yi zargin cewar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, dan asalin kasar Kamaru ne.

Kanu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a wani shiri da aka yada kai tsaye a London, kasar Ingila.

Kazalika, shugaban na IPOB ya zargi Atiku da jawo faduwar Alex Ekwueme a takarar kujerar shugaban kasa da ya yi a shekarar 1999.

Atiku ba dan Najeriya ba ne, shine ya kayar da Ekwueme zabe a 1999 - Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu
Asali: UGC

Kanu ya ce: “wasu daga cikin ku ba su san cewar Atiku ne ya yi sanadiyar faduwar Alex Ekwueme a zaben cikin gida na jam’iyyar PDP ba a lokacin da ya fito takara a 1999.”

Shugaban na IPOB ya gargadi ‘yan kabilar Igbo a kan kada kuri’a a zaben da za a yi cikin shekarar nan.

Kazalika, Kanu ya bayyana cewar ya gudu ya bar Najeriya ne a shekarar 2017 saboda sojoji na yunkurin hallaka shi.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta kama 'yan dabar siyasa da muggan makamai, hotuna

Na gudu ne saboda Buhari ya aika sojoji zuwa gida na domin su kasha ni saboda sun yi tsammanin sun fito domin gwabza fada da su. Bani da wani makami kamar yadda duk ragowar ‘yan kungiyar IPOB su ke,” a cewar Kanu.

Kanu na wadannan kalamai ne a matsayin martini ga ma su goranta ma sa cewar ya gudu ya bar dumbin magoya bayansa a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel