Zazzabin Lassa ya salwantar da rayukan Mutane 6, 40 sun kamu a jihar Filato

Zazzabin Lassa ya salwantar da rayukan Mutane 6, 40 sun kamu a jihar Filato

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu cewa, hatsabibiyar cutar nan mai sanya zazzabin Lassa ta silalo cikin Arewacin Najeriya inda rayukan mutane takwas suka salwanta. Cutar ta kuma harbi fiye da mutane 40 a jihar Filato.

Kwamishinan lafiya na jihar Filato, Dakta Kuden Kamshak, ya bayar da tabbacin yadda rayukan mutane takwas suka salwanta a sakamakon cutar zazzabin Lassa yayin da fiye da kimanin mutane arba'in suka kamu da ita.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Kamshak ya yi wannan karin haske a ranar Alhamis ta makon da ya gabata yayin wani taron sadarwa da kuma harkokin zamantakewa da aka gudanar cikin birnin Jos.

Zazzabin Lassa ya salwantar da rayukan Mutane 6, 40 sun kamu a jihar Filato
Zazzabin Lassa ya salwantar da rayukan Mutane 6, 40 sun kamu a jihar Filato
Asali: UGC

Masanin kiwon lafiyar ya misalta wannan lamari a matsayin babbar annoba da a halin yanzu gwamnatin jihar ta mike tsaye wurjanjan tare zage dantsen ta wajen dakile yaduwar cutar a fadin jihar.

Dakta Hamshak ya ce hukumomi masu ruwa da tsaki sun daura damara wajen aike da ma'aikatan lafiya shiyoyi daban-daban da ke fadin jihar domin tunkarar lamarin cikin gaggawa tare da kare lafiya gami da tsare rayukan al'umma.

Ya gargadi daukacin al'ummar jihar akan tsaftace muhallan su da wuraren mu'amala gami da gargadi akan barazanar da namun dawa musamman beraye da kuma jemagu ke haddasawa ga lafiyar Bil Adama.

KARANTA KUMA: Samun goyon bayan kungiyar dattawan Arewa da Kudu ta farantawa Atiku

Kazalika jagoran sadarwa a cibiyar lafiya ta kasa, Hajia January Bello, ta yi gargadi kan cewa al'umma su yi hattara da cutar Lassa domin kuwa ta na tarayya da cutar Ebola ta fuskar hatsari mai girman gaske.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, babban asibitin Murtala Muhammad da ke tantagwaryar birnin Kano, ya yi karin haske tare da jan kunnen al'umma dangane da barazanar cututtuka da rashin tsaftace muhalli ke haddasawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel