Sanatoci 24 da ba za su koma Kujerun su ba a bana

Sanatoci 24 da ba za su koma Kujerun su ba a bana

A yayin da lamari na rayuwa ya kan kasance yau gare ka gobe ga wanin ka, hakan tabbas za ta kasance ga wasu 'yan siyasa da dama da ke fadin kasar nan da ko shakka ba bu tun a yanzu sun fara bankwana da kujerun su na mulki.

Zauren majalisar dattawan Najeriya

Zauren majalisar dattawan Najeriya
Source: Depositphotos

Sakamakon jerin sunayen 'yan takara na karshe da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta fitar domin zaben kujerar shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu, akwai Sanatoci da dama da tun a yanzu sun san makomar su.

Cikin kaso 100 na 'yan majalisar dattawan Najeriya, akwai kaso 40 daga cikin su da tun a yanzu sun san makomar su ta rashin komawa bisa kujerun sa sakamakon rashin samun tikitin takara yayin zaben fidda, neman wasu kujerun daban, ko kuma wasu dalilai mabambanta juna ga kowane Sanata.

Akwai jerin mashahuran Sanatoci da da suka yanke shawarar ritaya daga kujerun su na majalisar dattawa domin wasu dama ta maye guraben su, yayin da wasunsu suka hakura da kujerun su domin hankoron kujerar gwamna ta jihohin su.

Cikin jerin mashahuran Sanatoci da suka yanke shawarar haramtawa kawunan su komawa bisa kujerun su na majalisar dattawa sakamakon a dade ana yi sai gaskiya da kuma wasu dalilai daban-daban sun hadar da;

1. Tsohon shugaban majalisar dattawa da ya shafe tsawon shekaru 20 a zauren majalisa; Sanata David Mark na jam'iyyar PDP mai wakilcin shiyyar Benuwe ta Kudu.

2. Tsohonn gwamnan jihar filato da ya shafe karo daya kacal a zauren majalisa; Sanata Jonah Jang na jam'iyyar PDP mai wakilcin shiyyar Filato ta Arewa.

3. Sanata Shaaba Lafiagi; na jam'iyyar PDP mai wakilcin shiyyar Kwara ta Arewa.

4. Sanata Demola Adeleke na jam'iyyar PDP mai wakilcin shiyyar Osun ta Yamma.

5. Tsohon gwamnan jihar Zamfara; Sanata Ahmed Sani na jam'iyyar APC mai wakilcin shiyyar Zamfara ta Gabas.

6. Sanata Bukar Abba na jam'iyyar APC mai wakilcin shiyyar Yobe ta Gabas.

7. Sanata Kaka Gabbai na jam'iyyar APC mai wakilcin shiyyar Borno ta Tsakiya.

8. Sanata Jerimiah Useni na jam'iyyar PDP mai wakilcin shiyyar Filato ta Kudu.

9. Tsohon gwamnan jihar Adamawa; Sanata Abdulaziz Murtala Nyako, na jam'iyyar ADC mai wakilcin shiyyar Adamawa ta Tsakiya.

10. Sanata Usman Bayero na jam'iyyar PDP mai wakilcin shiyyar Gombe ta Arewa.

11. Sanata Hope Uzodinma na jam'iyyar APC mai wakilcin shiyyar Imo ta Yamma.

12. Sanata John Enoh na jam'iyyar APC ma wakilcin shiyyar Cross River ta Tsakiya.

13. Sanata Gbenga Ashafa na jam'iyyar APC mai wakilcin shiyyar Legas ta Gabas.

14. Sanata Lanre Tejuoso na jam'iyyar APC mai wakilcin shiyyar Ogun ta Tsakiya.

KARANTA KUMA: Bayan rikotowar jirgi, Osinbajo ya gudanar da yakin neman zabe a jihar Kogi

15. Sanata Fatima Raji Rasaki ta jam'iyyar APC mai wakilcin shiyyar Ekiti ta Tsakiya.

16. Sanata Sola Adeyeye na jam'iyyar APC mai wakilcin shiyyar Osun ta Tsakiya.

17. Sanata Babajide Omoworar na jam'iyyar APC mai wakilcin shiyyar Osun ta Gabas.

18. Sanata Aliyu Sabi na jam'iyyar APC mai wakilcin shiyyar Neja ta Arewa.

19. Sanata David Umaru na jam'iyyar APC mai wakilcin shiyyar Neja ta Gabas.

20. Sanata Gilbert Nnaji na jam'iyyar PDP mai wakilcin shiyyar Enugu ta Gabas.

21. Sanata Emmanuel Paulker na jam'iyyar PDP mai wakilcin shiyyar Bayelsa ta Tsakiya.

22. Sanata Ben Murray Bruce na jam'iyyar PDP mai wakilcin shiyyar Bayelsa ta Yamma.

23. Sanata Fosta Ogala na jam'iyyar PDP mai wakilcin shiyyar Bayelsa ta Kudu.

24. Sanata Ahmed Abubakar na jam'iyyar APC mai wakilcin shiyyar Adamawa ta Yamma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel