Kar muke kallon kowa: Rabin mahalarta taron Buhari a Kano ba 'yan Nigeria ba ne - PDP

Kar muke kallon kowa: Rabin mahalarta taron Buhari a Kano ba 'yan Nigeria ba ne - PDP

- Jam'iyyar PDP ta zargi da jam'iyyar APC da dauko hayar dumbin jama'a daga kasar Niger domin su cika taron yakin neman zaben dan takararta na shugaban kasa a jihar Kano

- Jam'iyyar hamayyar ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhri ya kadu matuka bayan sanin irin aika-aikar da ta yi na hada wannan dumbin taro

- A cewar PDP, yanzu duniya ta san hanyar da shugaban kasar ya bi wajen samun kuri'u masu yawa a jihar a zaben 2015 da kuma yunkurin jam'iyyar na sama masa kuri'u 5m a 2019

Jam'iyyar adawa ta PDP ta zargi jam'iyyar APC da dauko sojojin haya daga kasar Niger domin su cika taron da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar na neman yakin zabensa a jihar Kano, wanda ya gudana ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu.

Jam'iyyar adawar ta sanar da wannan zargin nata ne a cikin wata sanarwa daga kakakin jam'iyyar, Kola Ologbondiyan, wacce aka rabawa manema labrai a daren ranar Alhamis, kamar dai yadda rahoton jaridar Vanguard ya bayyana.

Legit.ng Hausa ta tattaro rahoto kan cewa, PDP ta ce ya zama wajibi ace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kadu matuka idan ya san cewa jam'iyyarsa ta dauko hayar wasu mutane ne masu yawa domin su cika taron yakin zaben nasa, bayan da masu shirya taron suka gaza hada kan jama'ar Kano da za su halarci taron.

KARANTA WANNAN: Iyaye mata kuyi hattara: An gano sinadarai masu guba a cikin nafkin din yara

Kar muke kallon kowa: Rabin mahalarta taron Buhari a Kano ba 'yan Nigeria ba ne - PDP
Kar muke kallon kowa: Rabin mahalarta taron Buhari a Kano ba 'yan Nigeria ba ne - PDP
Asali: Facebook

Sanarwar ta ce: "Yan Nigeria sun ga yadda gwamnoni biyu da kuma wani babban basarake daga jamhuriyyar Niger suka halarci taron, wadanda aka baiwa kwangilar shigowa da jama'arsu kasar domin halartar taron.

"Jama'a sunga yadda mahalarta taron suka kasa kama kansu da kuma banbance banbancen kalolin jikinsu, haka zalika, sun kasa amsa kuwwar jawaban shuwagabannin APC, amma dai sun ci gaba da dambarwa wanda ya tilasta aka rinka sanar da su abubuwan da zasu fada a wajen taron.

"A yanzu duniya ta san hanyar da shugaban kasa Buhari ya bi wajen samun kuri'un da ya samu a Kano a zaben 2015 da kuma hanyar da jam'iyyar za ta fi wajen sama masa kuri'u miliyan 5 a zaben 2019 kamar yadda gwamnan jihar ya yi alkawari."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel