Makashin maza: Yadda Yansanda suka kashe wani bijimin dan fashi da makami

Makashin maza: Yadda Yansanda suka kashe wani bijimin dan fashi da makami

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya sun samu nasarar kashe wani kasurgumin jagoran yan fashi da makami a jahar Enugu yayin da suka kaddamar da samame akan gungun yan fashin da yake jagoranta.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin yansandan jahar, SP Ebere Amaraizu ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu, inda yace gungun yan fashin sun saba tare hanyar 9th Mile-Udi-Oji-Awka suna yi ma matafiya fashi.

KU KARANTA: Naka naka ne: Buhari ya amince da kashe N91,000,000,000 domin amfanin Fulani

Dubun wadannan miyagun mutane ta cika ne a ranar Laraba, 30 ga watan Janairu a lokacin da Yansanda suka kai musu harin kwantan bauna da misalin karfe 3 na dare a daidai babbar hanyar Agungwu, inda suka kashe jagoransu, sauran kuma suka tsere da raunukan harsashi.

“Mun samu bayanan sirri dake nuna cewa yan fashin sun yi kwamba sun sanya shingen binciken ababen hawa akan titin ne, daga nan ne muka bazama farautarsu, isanmu keda wuya sai suka bude mana wuta, anan muma muka fara mayar da wuta.

“A sanadiyyar musayar wutan ne muka kashe guda daga cikin jagororin yan fashin kamar yadda likitoci suka tabbatar mana a asibiti, yayin da sauran suka tsere, amma fa suna dauke da raunuka da suka samu a sanadiyyar harbe harben bindigan Yansanda.” Inji shi.

Da wannan ne ake kira ga duk wanda ya ga wani mutumi dauke da mummunan rauni irin wanda harsashi ke sanyawa a gida ko a asibiti daya yi gaggawar sanar da rundunar Yansanda ko kuma wata hukuma mafi kusa.

Daga karshe Kaakakin yace sun kaddamar da cikakken bincike akan yan fashin, sa’annan suna farautar yan bindigan ruwa a jallo, musamman a yankin tafkin Oji da yankunan dake makwabtaka da shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel