Naka sai naka: Buhari ya amince da kashe N91,000,000,000 domin amfanin Fulani

Naka sai naka: Buhari ya amince da kashe N91,000,000,000 domin amfanin Fulani

Gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da kashe naira biliyan casa’in da daya a wani tsarin samar da gandun kiwo ga Fulani makiyaya da sauran masu kiwon dabbobi a Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ana sa ran wannan tsarin zai dauki tsawon shekaru goma, sa’annan zai samar da ribar da ta haura naira Tiriliyan biya, makasudin shirin shine kawo karshen rikice rikicen makiyaya da manoma.

KU KARANTA: Zan dauki tsatstsauran matakai akan kwamandojin rundunar Sojin Najeriya –Atiku

Naka naka ne: Buhari ya amince da kashe N91,000,000,000 domin amfanin Fulani

Gandun kiwo
Source: UGC

Kashin farko na shirin zai mayar da hankali ne zuwa gandun kiwo dake jihohi guda bakwai na Arewacin Najeriya da suka fi fuskantar rikicin makiyaya da manoma domin basu kulawar da ta dace, jihohin sun hada da Adamawa, Benue, Kaduna, Nasarawa, Plateau, Taraba, da Zamfara.

A karkashin wannan tsari da gwamnatin Buhari ta bullo dashi, za’a dinga baiwa dabbobi irin abincin zamani domin su kara nauyi daga kilo 200 zuwa kilo 500, wanda hakan zai kara musu girma, karin nono da kuma riba mai yawa.

Shi dai wannan tsari ya tanadi yarjejeniya tsakanin makiyaya da ma’aikatan gandun, ta yadda idan har aka shigar da dabba cikin wannan tsarin, makiyayi zai amince a sayar da dabbarsa bayan an kammala mata aiki akan naira dubu tara akan kowanni kilo, daga nan sai gwamnati ta zare kudinta ta mika ma makiyayi sauran kudin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel