Kwarewa ta akan siyasa da kasuwanci ya sanya na ke takarar kujerar shugaban kasa - Atiku

Kwarewa ta akan siyasa da kasuwanci ya sanya na ke takarar kujerar shugaban kasa - Atiku

- Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya ce kwarewar sa akan siyasa da kasuwanci ya sanya ya ke takarar kujerar shugaban kasa

- Atiku ya halarci taron sauraron ra'ayin al'umma a garin Abuja, ya amsa tamboyi da dama

- Waziri Adamawa ya ce gwamnatin shugaban Buhari ta gaza samar da ingantaccen tsaro a yankunan Arewa na Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce kwarewar sa gami da yalwar ilimi akan harkoki siyasa da kuma kasuwanci ya sanya ya ke takarar kujerar shugaban kasar Najeriya domin fidda ita zuwa tudun tsira.

Kwarewa ta akan siyasa da kasuwanci ya sanya na ke takarar kujerar shugaban kasa - Atiku
Kwarewa ta akan siyasa da kasuwanci ya sanya na ke takarar kujerar shugaban kasa - Atiku
Asali: Twitter

Wazirin Adamawa ya ce, babban dalilin da ya sanya ya ke hankoron kujerar shugaban kasa bai wuci cikar burin sa ba na yada kwarewar sa ta siyasa da kuma harkokin kasuwanci a yayin da ya ke rike da akala ta jagorancin kasar nan.

Atiku ya bayyana hakan ne a yau Laraba yayin zaman sauraron ra'ayin al'umma da aka gudanar a babban Otel din Sheraton da ke garin Abuja. Ya ce zai kasance tamkar tsani na cike gurbin da ke tsakanin al'ummar yanzu da kuma ta zamanin gaba.

KARANTA KUMA: 2019: Atiku ya yi nadama, ya tuba - Obasanjo

Baya ga kasancewar sa mafi cancanta cikin dukkanin 'yan takara da ke neman kujerar shugaban kasa a zaben bana, Atiku ya ce yana da muradin al'ummar Najeriya su ci gajiya da kuma ribar kwarewar sa akan harkokin siyasa da kuma kasuwanci.

Turakin Adamawa ya kuma bayyana takaicin sa dangane da yadda rikon sakainar kashi ta gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi tasiri wajen ci gaba da yaduwar barazana da kuma kalubalen tsaro da ake fuskanta musamman a Arewacin Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel