Atiku, Buhari za su halarci taron kungiyar Izala na kasa a Abuja - JIBWIS

Atiku, Buhari za su halarci taron kungiyar Izala na kasa a Abuja - JIBWIS

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, za su halarci wani babban taro na addini a garin Abuja.

Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa'ikamatis Sunna, JIBWIS, ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, za su halarci babban taron ta na kasa da za a gudanar babban birnin kasar nan na tarayya.

Rahotanni sun bayyana cewa, taron da za a gudanar a ranar Lahadi ta karshen wannan mako zai gudana ne da manufa ta neman gudunmuwa da kuma tallafi na sayen kayayyakin aikace-aikace domin kafa wata sabuwar cibiyar ilimi ta kimanin Naira Miliyan 250.

Atiku, Buhari za su halarci taron kungiyar Izala na kasa a Abuja - JIBWIS

Atiku, Buhari za su halarci taron kungiyar Izala na kasa a Abuja - JIBWIS
Source: Facebook

Kungiyar JIBWIS ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sa hannun babban sakataren ta akan hulda da al'umma, Ahmad Muhammad Ashiru. Ya ce babban taron zai gudana a tsohuwar harabar Fareti da ke garin Abuja.

KARANTA KUMA: Yakin Zabe: Buhari ya ziyarci jihar Ebonyi

Sauran jiga-jigan da ake sa ran za su halarci babban taron sun hadar da Gwamnoni, Ministoci, Sanatoci, 'yan Majalisar wakilai, hamshakan attajirai da 'yan kasuwa, da kuma fitattun 'yan siyasa da suka shahara a fadin kasar nan.

Cikin wani rahoton da shafin jaridar Legit.ng ya ruwaito ta bayyana cewa, rundunar sojin sama ta Najeriya ta yi luguden wuta kan wani sansanin masu tayar da kayar baya na Boko Haram a jihar Borno.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel