Kyautar manyan motoci: Sheikh Bala Lau ya kare kan sa

Kyautar manyan motoci: Sheikh Bala Lau ya kare kan sa

- A satin da ya gabata ne shugaban kungiyar Izala ta kasa (JIBWIS), Sheikh Bala Lau, ya nemi mambobi da magoya bayan kungiyarda su zabi shugaba Buhari a zabe mai zuwa

- Bayan furucin na shugabannin kungiyar ta Izala ne rahotanni su ka bayyana cewar gwamnan jihar Kaduna ya bawa Sheikh Lau kyautar wasu motocin alfarma

- Sai dai a wani jawabi da kungiyar Izala ta fitar, Sheikh Bala Lau, ya karyata rahotannin da ke cewar an bashi kyautar mota

Shugaban kungiyar Izala ta kasa (JIBWIS), Sheikh Bala Lau, ya kalubalanci gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El_Rufa'i, da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da su fito su bayyana lokacin da su ka bashi kyautar mota.

A wata sanarwa da kungiyar JIBWIS ta fitar a shafinta na yanar gizo, Sheikh Bala Lau, ya karyata rahotannin da ke yawo a gari kan cewar gwamnan jihar Kaduna ya bashi kyautar wasu mayan motoci na alfarma saboda ya nemi mambobinsu su zabi Buhari.

Kyautar manyan motoci: Sheikh Bala Lau ya kare kan sa
Sheikh Bala Lau
Asali: Twitter

A makon da ya gabata ne shugaban kungiyar ta Izala ya nemi mambobinsu da magoya baya da su kada kuri'un su ga shugaba Buhari a zabe mai zuwa.

DUBA WANNAN: Rundunar sojin ruwa ta fara shirin daukar sabbin ma'aikata na shekarar 2019

Sai dai, bayan Sheikh Lau ya yi wannan furuci ne rahotanni su ka bayyana cewar El-Rufa'i ya bahi kyautar motoci saboda yiwa Buhari kamfen.

Da yake kare kansa a kan wannan zargi, Sheikh Lau ya ce zancen, zuki ta malle ce kawai tare da fadin cewar, "kowa ya yi da kyau ya sani."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel