Rundunar sojin ruwa ta fara shirin daukar sabbin ma'aikata na shekarar 2019

Rundunar sojin ruwa ta fara shirin daukar sabbin ma'aikata na shekarar 2019

Rundunar sojin ruwa ta kasa ta sanar da fara karbar takardun masu sha'awar fara aiki da su a cikin wannan shekarar, 2019, kamar yadda sanarwar da darektan yada labarai na rundunar, Suleman Dahun, ya fitar a yau, Lahadi, a Abuja.

Ya ce masu sha'awar neman aiki a rundunar sojin ta ruwa zasu iya aika takardun su na karatu da cike fom din neman aiki a shafin yanar gizo na rundunar kamar haka; www.joinnigeriannavy.com

Mista Dahun, mai mukamin kwamanda, ya ce duk masu sha'awar aiki da rundunar sojin ruwa dole ya kasance sun ci jarrabawar kammala makarantar sakandire a darussa 5 da suka hada harshen turanci da lissafi.

Ya kara da cewa ana bukatar masu shekaru 18 zuwa 22 ne a rukunin kananan sojoji da kuma shekaru 24 zuwa 26 a bangaren tsaka-tsakin jami'an soji da ke da shaidar kammala karatun Difloma da NCE.

Rundunar sojin ruwa ta fara shirin daukar sabbin ma'aikata na shekarar 2019
Dakarun rundunar sojin ruwa
Asali: UGC

"Babu bukatar ma su takardun shaidar kammala karatu fiye da wadan nan da mu ka ambata su nemi aikin.

"Marasa aure ne kawai zasu iya samun gurbin aiki a wannan rukuni, kuma dole su kasance haifaffun 'yan Najeriya da tsayin su bai gaza 1.7m ga maza da 1.67 ga mata," a cewar sa.

Ya shawarci ma su neman aiki da su guji bayar da kudi ga wani mutum ko wata kungiya da sunan zasu taimake su wajen samun aiki da rundunar sojin ruwa.

DUBA WANNAN: INEC ta yi barazanar korar wasu ma'aikatan hukumar

"Yana da kyau na jawo hankalin ma su neman aiki da kar su kuskura su bawa wani mutum ko wata kungiya kudi da sunan za su taimaka ma su wajen samun gurbin aiki a rundunar sojin ruwa.

"Duk wanda aka gano ya yi karyar takardun karatu za a mika shi hannun rundunar 'yan sanda domin daukan matakin shari'a a kan sa ko a kan ta," kamar yadda Dahun ya fada

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel