An karrama mutane 6 da suka nuna halaye irin na Sir Ahmadu Bello Sardauna a Kaduna

An karrama mutane 6 da suka nuna halaye irin na Sir Ahmadu Bello Sardauna a Kaduna

Masu iya magana na cewa “hali zanen duste”, da wannan ne gidauniyar tunawa da tsohon firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardauna ta karrama wasu yan Najeriya guda shida da suka nuna wasu kyawawan halaye irin na Sardauna.

Sanannen lamari ne cewa Sardauna a zamaninsa ya kwatanta adalci a mulki, ya tausaya ma talaka, ya yi gwagwarmayar yantar da mutumin Arewa, haka zalika bai nuna banbamci ga sauran kabilu ko mabiya addinai dake Arewa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin wadanda aka karrama akwai Abubakar Abdullahi, limamin nan daya tseratar da kiristoci guda dari uku (300) daga harin yan bindiga, inda ya boyesu a cikin Masallacin da yake limanci a kauyen Ngahr cikin garin Barikin Ladi na jahar Filato.

KU KARANTA: Shugaban jam’iyyar APC yace Buhari zai yafe ma duk dan siyasar da ya dawo jam’iyyar APC

An karrama mutane 6 da suka nuna halaye irin na Sir Ahmadu Bello Sardauna a Kaduna

Idowu, Liman Abubakar da Uwais
Source: UGC

Sauran mutanen da suka samu karramawa daga gidauniyar Sardauna sun hada da tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Mai sharia Muhammad Lawal Uwais, sakataren kungiyar kiristoci mabiya darikar katolika ta duniya gaba daya, Idowu Fearon.

Sai kuma Abdullahi Abubakar na jami’ar Ahmadu Bello daga tsangayar kimiyyar hada magunguna, Dakta Lateef Taiwo Sheikh da kuma babban basaraken al’ummar kabilar Marwa ta jahar Kaduna, Dakta Tagwai Sambo.

Gidauniyar ta bayyana cewa ta karrama mutanen shida ne sakamakon gudunmuwar da suke bayarwa wajen samun dawwamammen zaman lafiya a Najeriya, inda tace ta karrama Uwais ne saboda gudunmuwarsa ga hidimar jama’a.

Yayin da Idowu Fearon ya samu lambar yabo saboda kokarin da yake yi na samar da zaman lafiya, shi kuwa Liman Abubakar ya samu karramawa ne saboda rawar daya taka wajen isar da sakon addinin musulunci na mutunta ran dan adam, kauna da martaba mutum.

Da yake mika musu lambobin karramawar, shugaban gidauniyar, Galadiman Katsina, hakimin Malumfashi, Mai sharia Mamman Nasir ya bayyana cewa sun karrama mutanen ne a matsayin gudunmuwarsu ga inganta rayuwar dan adam a Arewa da Najeriya gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel