Satan dan kamfen mata: Wani mutum ya sha da kyar a hannun fusatattun matasa

Satan dan kamfen mata: Wani mutum ya sha da kyar a hannun fusatattun matasa

Kiris ya rage wasu fusattatun matasa su kashe wani mutum mai matsakaicin shekaru da aka kama yana satan da dan kamfen mata a Mgabkwu da ke karamar hukumar Awka ta Arewa na jihar Anambra.

An cafke mutumin ne mai suna Ifeanyi dan asalin jihar Enugu a harabar dakunnan dalibai mata inda ya ke yunkurin sace musu dan kamfai domin ya tafi ya sayar.

The Nation ta gano cewa mutumin ya amsa cewar ya sace dan kamfai sama da 58 kafin asirinsa ya tonu a asubahin ranar da wata budurwa ta kama shi.

Satan dan kamfen mata: Wani mutum ya sha da kyar a hannun fusattatun matasa
Satan dan kamfen mata: Wani mutum ya sha da kyar a hannun fusattatun matasa
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Jihohi 10 da suka fi bunkasa a Najeriya a yanzu

Wani mazaunin unguwar da ya nemi a boye sunansa ya ce wanda ake zargin ya shiga harabar dakunnan 'yan matan ne misalin karfe 2 na dare.

Ya ce, "Ya wuce igiyar shanya inda matan suka bar kamfensu ya bushe ya fara kwasa kwatsam sai wata mace da ta fito fitsari ta gan shi kuma tayi ihun barawo.

"Daga nan ne makwabta suka fito suka yi masa zigidir suka nakada masa duka."

Majiyar Legit.ng ta cewa wanda ake zargin ya ce ya dade yana wannan mummunar aikin kuma ya roki mutanen su sasauta masa.

"Na san sayar wa wani Emeka Ofor ne a Enugu kan farashin N500 kowanne guda," inji shi.

Daga bisani ya ce shaidan ne jefa cikin wannan mummunan sana'ar.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya ce ba shi da labarin afkuwar lamarin a lokacin da ake hada wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel